Tirkashi: SERAP Ta Mika Babbar Bukata ga Tinubu, Atiku da Sauran 'Yan Takara a Zaben 2027

Tirkashi: SERAP Ta Mika Babbar Bukata ga Tinubu, Atiku da Sauran 'Yan Takara a Zaben 2027

  • SERAP ta bukaci ’yan takarar shugaban kasa 19 da INEC ta sanar su bayyana kadarorinsu da basussukansu gabanin zaben 2027
  • Kungiyar ta kuma bukaci ’yan takarar su bayyana halastattun hanyoyin da suka samo manyan kadarorinsu
  • SERAP ta bukaci ’yan takarar su yi watsi da sayen kuri’u da cin hanci a zaben shekarar 2027 da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar SERAP ta mika bukatarta ga dukkanin 'yan takarar shugaban kasa 19 da INEC ta sanar.

SERAP ta bukaci dukkan ’yan takarar su bayyana bayanan kadarorinsu da basussukansu, da na matansu ko mazajensu, da kuma ’ya’yansu da ba su kai shekara 18 ba kuma ba su yi aure ba, gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

SERAP ta mika bukatarta ga Tinubu, Atiku
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya fitar, inda ta ce an gabatar da bukatar cikin wata wasika da aka aikawa ’yan takarar mai kwanan wata 8 ga Agusta, 2026, cewar rahoton jaridar The Punch

Kara karanta wannan

Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa

SERAP ta kuma bukaci ’yan takarar su bayyana halastattun hanyoyin da suka samo manyan kadarorinsu tare da yin watsi da sayen kuri’u da cin hanci a zabe kafin da kuma lokacin zaben.

’Yan takarar da SERAP ta lissafa

’Yan takarar 19 da SERAP ta ambata sun hada da Shugaba Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na ADC; Peter Obi na NDC; Sanata Sandy Onor na PDP; Omoyele Sowore na AAC, Donald Duke na PRP; Okwori Ada Elizabeth Frederick ta NDP; Chukwu Anita Zugwai na YPP; Rufai Adekunle Omoaje na AA; da Adenuga Sunday na Boot Party.

Sauran sun hada da Memeh Samuel na Democratic Labour Alliance; Nwanyanwu Daniel Danerechukwu na ZLP; Okereke Sunday Chibuzor na LP; Okereke Iken Esther na NRM; Abbas-Bin Aliyu na ADP; Dikwa Suleiman Mohammed na NNPP; Adebayo Adewole Ebenezer na SDP; Seyi Makinde na APM; da Yusuf Kabiru na APP.

SERAP ta bukaci ’yan takarar da su “wuce abin da doka ta tanada kawai, su rungumi manyan ka’idojin gaskiya, rikon amana da nagarta” yayin neman shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: APC ta ɗora sunayen yan takarar gwamna da mataimakansu a shafin INEC

Kungiyar ta ce ’yan takarar da ke neman ’yan Najeriya su damka musu manyan iko na kundin tsarin mulki kan kudaden gwamnati, albarkatun kasa, nade-naden mukamai da hukumomin tsaro ya kamata su kasance a shirye, kafin neman kuri’u, su nuna cewa harkokin kudinsu na kashin kansu za su iya jure binciken jama’a mai ma’ana.

SERAP ta yi magana kan zabe

SERAP ta ce dimokuradiyyar Najeriya ta ’yan kasar ce, don haka bai kamata a sayi kuri’u ko a mayar da mukamin gwamnati dukiyar kashin kai ba, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Kungiyar ta ce masu neman mukamin shugaban kasa ya kamata su kasance a shirye su cika mafi girman ka’idojin gaskiya, rikon amana da nagarta.

Ta kara da cewa zaben shugaban kasa na 2027 wata dama ce ga shugabannin siyasa su nuna cewa mukamin gwamnati amana ce da jama’a suka ba su.

SERAP ta ce ’yan takarar da suka bayyana kadarorinsu da kansu tare da yin watsi da sayen kuri’u za su iya nuna cewa a shirye suke su tabbatar da gaskiya da rikon amana da suka yi alkawarin samarwa idan aka zabe su.

Abin da kundin tsarin mulki ya tanada

Kungiyar ta lura cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi kai tsaye cewa ’yan takarar shugaban kasa su wallafa bayanan kadarorinsu kafin zabe ba.

Kara karanta wannan

Annoba mai alaka da kudaje ta barke a Bauchi, mutane sun fara mutuwa

Sai dai SERAP ta ce kundin tsarin mulkin ya kunshi ka’idojin gaskiya, rikon amana da nagarta wajen rike mukaman gwamnati.

SERAP ta ce kundin tsarin mulkin ya riga ya bukaci zababbun jami’an gwamnati, ciki har da shugaban kasa, su bayyana kadarorinsu da basussukansu.

An bukaci Obi ya bayyana kadarorinsa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027 Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Sarki na son hana Obi da Atiku kamfe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani lauya, Damilare Adenola, ya soki sanarwar Oluwo na Iwoland, Oba Abdulrosheed Akanbi kan yakin neman zaben shugaban kasa.

Hakan na zuwa ne bayan an ji Sarkin na cewa babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kamata ya yi yakin neman zaɓe a Osun kafin babban zaɓen 2027, sai Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng