2027: Masu Neman Takara Sun Cika Sakatariyar APC da Gidan Shugaban Jam'iyya
- Rahoto ya nuna cewa masu neman takara a APC sun cika sakatariyar jam’iyyar da gidan Farfesa Nentawe Yilwatda a birnin tarayya Abuja
- Lamarin ya sa an fara zargin cewa wasu masu neman takara ke hasashen ba za su samu tikitn jam'iyyar ba ne suka hallara wajen
- Wani rahoto ya nuna cewa masu neman tikitin takarar majalisar wakilai sun fi nuna damuwa saboda zaɓen tsaida gwaninsu ne na farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masu neman takara sun cika sakatariyar jam’iyya da gidan shugaban APC na kasa domin jiran sakamakon tantance su da aka yi.
Tarin masu neman takara da wakilansu sun cika babbar sakatariyar jam’iyyar APC jiya, suna jiran fitar da rahoton kwamitin tantance su da jam’iyyar ta kafa.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa ana sa ran kwamitin tantancewar zai fitar da sunayen waɗanda suka yi nasarar samun damar shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a ranar Alhamis.
An mamaye sakatariyar jam'iyar APC
Masu neman takarar da suka isa sakatariyar jam’iyyar tun ƙarfe 8:00 na safe sun jira har ƙarshen lokacin aiki domin a fitar da rahoton tantance su.
Da aka kasa fitar da rahoton bayan ƙarewar lokacin aiki, sai suka nufi gidan shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
APC ta bayyana cewa ranakun da aka tsara domin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027 ba su canja ba.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar, ya ce dole ne a yi ƙarin haske bayan yaɗuwar rahotannin ƙarya da masu ruɗarwa a kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa da ke nuna akasin haka.

Source: Facebook
Lokacin zaben fitar da gwanin APC
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Morka ya ce kamar yadda aka sanar tun farko, zaɓen fidda gwani zai gudana kamar haka:
Na Majalisar Wakilai — Juma’a, 15 ga Mayu, 2026,
Na Majalisar Dattawa — Litinin, 18 ga Mayu, 2026,
Na Majalisun Dokokin Jihohi — Laraba, 20 ga Mayu, 2026.
Zaɓen fitar da gwani na gwamna zai gudana ranar Alhamis, 21 ga Mayun 2026, yayin da na shugaban ƙasa zai gudana ranar Asabar, 23 ga Mayun 2026.
Bisa jadawalin da jam’iyyar ta fitar tun farko, an tsara fitar da sakamakon tantancewar ranar Talata, amma har lokacin hada wannan rahoton a ranar Alhamis ba a fitar da shi ba.
Jigon APC ya tayar da kura
A wani labarin, kun ji cewa, mai neman takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a Taraba, David Sabo Kente ya bukaci a masa adalci.
David Sabo Kente ya bayyana cewa ya samu karbuwa a wajen masu ruwa da tsaki a fadin jihar, kuma saboda haka ne ma suka saya masa fom din neman takara.
A karkashin haka, dan siyasar ya bayyana cewa adalci wajen zaben fitar da gwani ne kawai zai kawo zaman lafiya a cikin jam'iyyar APC a Taraba.
Asali: Legit.ng

