Kwanaki 10 kafin a Fara Kamfen, Sabani Ya Shiga tsakanin Atiku da ADC
- Kasa da kwanaki 10 suka rage kafin fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2027, ana neman tayar da kura game da mai yi wa Atiku kamfen
- Wasu rahotannu sun ce ADC da dan takararta Atiku Abubakar sun samu sabani kan wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zabensa
- Ana ganin tsagi daya ya karkata ga tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kasa da kwanaki 10 suka rage kafin fara yakin neman zaben shugaban kasa gabanin babban zaben 2027, amma rikici na neman shigowa ADC.
Rahotanni sun ce jam’iyyar adawa ta ADC da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun samu sabani kan wanda ya kamata ya jagoranci yakin neman zabensa.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Source: Twitter
Labarin da ya kebanta da The Guadian ya bayyana cewa wannan batu na zuwa ne a yayin da kungiyoyin fararen hula da wasu ‘yan majalisa ke kara yin kira da a yi garambawul ga tsarin zabe tare da tabbatar da karin gaskiya da rikon amana gabanin zaben 2027.
Ana samun sabani a ADC
Rahotanni sun ce sabanin da ake samu a ADC ya fi karkata ne kan tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke.

Source: Facebook
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranar 19 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2027.
Gabanin wannan rana, jam’iyyun siyasa sun fara kammala shirye-shiryen kafa tsarin yakin neman zabensu, duk da cewa ba dole ba ne jam’iyyun su fara yakin neman zabe a rana guda.
ADC, APC da sauran jam'iyyu sun fara shiri
Ana sa ran manyan jam’iyyun siyasa, wato APC, ADC,N DC da PDP, za su bayyana tawagogin yakin neman zaben shugaban kasa kafin ranar fara yakin neman zaben, domin nuna shirinsu na tunkarar zaben.
Sai dai ADC, wadda ake kara kallonta a matsayin babbar jam’iyyar da za ta iya taka muhimmiyar rawa a zaben 2027, na cikin wani sabani kan ko Tambuwal ko Imoke ne ya kamata ya jagoranci yakin neman zaben Atiku.
Rahotannin sun bayyana wannan al'amarin da kutso cikin ADC ya fara jefa rabuwar kai tsakanin yankunan kasar nan gabanin fara kamfen.
Wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun ce Atiku da wasu mambobin NWC daga sassa daban-daban na kasar na goyon bayan Tambuwal ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben.
Sai dai wasu na matsa lamba a bai wa dan siyasar Kudu, musamman Imoke, damar jagorantar yakin neman zaben shugaban kasa.
ADC ta tura sako ga Tinubu
A baya, mun kawo labarin cewa ADC ta ce umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa EFCC ya nuna hukumar ba ta da cikakken 'yancin gudanar da aikinta kamar yadda ya yi ikirari.

Kara karanta wannan
'Atiku da Amaechi, Peter Obi da Kwankwaso ba za su iya samun nasara a zaben 2027 ba'
Jam'iyyar ta kalubalanci ikirarin cewa akwai umarnin kotu da EFCC ta dogara da shi wajen dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun ana saura makonni kadan a gudanar da zabe.
Jam'iyyar hamayya ta ADC ta bukaci Tinubu ya yi irin wannan katsalandan a shari'ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai idan da gaske yana son adalci ta tabbata a mulkinsa.
Asali: Legit.ng
