Tinubu Ya Aika Sako ga 'Yan APC ana Shirin Fara Zaben Fitar da Gwani
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga mambobin APC yayin da ake shirin fara zaben fitar da gwani
- Mai girma Bola Tinubu ya bukaci mambobin APC da masu neman takara da su nuna halin dattako yayin da ake shirin fara zaben fitar da gwanin
- Shugaban kasar ya bukaci su ba 'yan adawa kunya ta hanyar kin tayar da rikici a zabubbukan fitar da gwanin na jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya aika sako ga mambobi, masu neman takara da shugabannin jam'iyyar APC.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga mambobi, masu neman takara, da shugabannin jam’iyyar APC da su nuna halin dattako yayin da za a fara gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.
Shugaba Tinubu ya ja kunnen 'yan APC
Tinubu ya fitar da sanarwar ne ana sauran kwana daya a fara zaben fitar da gwani na Majalisar wakilai na jam'iyyar APC, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
Tinubu ya yi gargaɗin cewa halayyar tada rikici ba za ta amfani kowa ba sai ’yan adawa, sannan ya gargaɗi waɗanda suka yi nasara da kada su nuna izza, yayin da ya buƙaci waɗanda suka sha kaye da su karɓi ƙaddara cikin girma.
Shugaba Tinubu ya ce waɗannan ayyukan ba wai kawai fage ne na samar da ’yan takara ba, a’a, jarrabawa ce ga haɗin kan APC, juriya, da kuma ƙarfin jam’iyyar yayin da take shiga kakar zaɓe ta huɗu.
“A kowace takara, dole ne a samu wanda zai yi nasara da wanda zai sha kaye. Ina kira ga waɗanda suka yi nasara da kada su rura wuta don murna, su kuma waɗanda suka sha kaye su nuna halin girma ta hanyar karɓar abin da ya faru da natsuwa tare da shirin wani lokacin.”
“Manyan waɗanda suka yi nasara su ne waɗanda ba sa zaɓi ruguza tafiyar ba, sai dai su yi aiki don tunkarar wani zagayen. Masu adawa da mu suna jiran mu yi fada da juna; ya kamata mu ba su kunya.”
- Shugaba Bola Tinubu
Wace shawara Tinubu ya ba da?
Shugaban ya yi nuni da salon siyasar da ya ce jam’iyyar ta riga ta bari a baya, inda ya ambato hakan ne musamman don yin gargaɗi kan dawowarsa.
“Kada mu yi siyasar da ake yi a baya, siyasar nan ta ‘mutu-ka-raba’ da muka riga muka bari a baya.”
“Kada siyasa ta zama wasan rashi ga ɗaya, riba ga ɗaya. Duk ɗan takarar da ya yi nasara, ya yi nasara ne ga dukkanmu a matsayinmu na jam’iyya."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Tinubu ya ce a duk inda aka riga aka cimma matsaya ta maslaha a tsakanin masu neman takara, ya kamata a yi amfani da hakan sosai don rage saɓani.
Tsohon gwamna ya shiga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Olusegun Mimiko wanda ya yi gwamna sau biyu a jere a jihar Ondo, ya sauya sheka zuwa APC ne bayan ficewa daga jam'iyyar PDP.
Mimiko ya bayyana cewa rawar da Shugaba Bola Tinubu yake takawa ce ta yi tasiri ga shawararsa ta komawa jam’iyya mai mulki.
Asali: Legit.ng

