APC Ta Fitar da Dan Takarar Gwamna a Oyo, Ta Juyawa Ministan Tinubu Baya

APC Ta Fitar da Dan Takarar Gwamna a Oyo, Ta Juyawa Ministan Tinubu Baya

  • APC a Jihar Oyo ta hada kai wajen goyon bayan Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna a da zai wakilce ta a babban zaben 2027
  • Hakan na zuwa ne yayin da jihohin da jam'iyyar APC ke mulki a Najeriya ke kokarin fitar da wadanda za su masu takara a zabe mai zuwa
  • Ministan makamashi da ya yi murabus daga gwamnatin Bola Tinubu, Bayo Adelabu bai samu goyon bayan jam'iyyar APC ba a jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Oyo sun amince da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027.

A ranar Juma’a APC ta amince da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen shekara mai zuwa, lamarin da ke nuna tsohon ministan makamashi bai samu shiga ba.

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Sharafadeen Alli
Sharafadeen Alli da APC ta goyi bayansa a Oyo. Hoto: Oyo Matters
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa an tabbatar da haka ne a wani babban taron da aka gudanar a Ibadan, inda jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar suka hallara domin tattauna dabarun zaben 2027.

APC ta zabi dan takara a Oyo

Da yake jawabi a taron, Sanata Ayo Adeseun ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tabbatar da takarar Sanata Alli da kuma samar da hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, wannan shawara ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi, kuma ta samu karin karfi da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa, Adeseun ya ce ya taba ganawa da Shugaban a Abuja, inda aka ce Tinubu ya bayar da hujjoji masu karfi na goyon bayan Alli a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyyar a Jihar Oyo.

The Cable ta rahoto cewa y jaddada cewa a matsayinsa na jagoran kasa na APC, ra’ayin Shugaban yana da muhimmanci sosai kuma ya kamata mambobin jam’iyyar su girmama shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni da 'yan APC sun fitar da dan takarar gwamnan Yobe a 2027

Taswirar jihar Oyo
Taswirar jihar Oyo a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Haka kuma, wani jigo na jam’iyyar, Alhaji Fatai Ibikunle, ya sake jaddada matsayar shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa shi ma ya gana da Shugaba Tinubu, wanda ya amince da Alli a matsayin wanda ya fi dacewa da tikitin 2027 a Jihar Oyo.

Ga bidiyon bayanin da shugabannin APC suka yi da shafin Oyo Matters ya wallafa a X:

Bayanin dan takarar APC a Oyo

A nasa jawabin, Sanata Alli ya gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar bisa goyon bayan da suka nuna masa, yana mai alkawarin gudanar da shugabanci mai kyau.

Ya tabbatar wa shugabanni da mambobin jam’iyyar cewa ba zai basu kunya ba, yana kuma gode wa Shugaban kasa bisa jagoranci mai kyau da yake bai wa jam’iyyar a jihar.

Maganar takarar Bayo Adelabu

A wani labarin, mun kawo muku cewa ministan makamashi, Bayo Adelabu ya tabbatar da cewa zai nemi takarar gwamna a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƴan sanda ya ƙi yarda da sulhu, ya sayi fom ɗin takarar gwamna

Bayo Adelabu ya karyata cewa bai samu goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba, inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya masa fatan alheri a lokacin da ya gana da shi a fadar shugaban kasa kan maganar takara da murabus dinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng