Mai Son Takarar Gwamna Ya Yi Gargadin Tarwatsewar APC a Taraba

Mai Son Takarar Gwamna Ya Yi Gargadin Tarwatsewar APC a Taraba

  • Fitaccen mai neman takarar gwamna na APC a jihar Taraba, David Sabo Kente, ya yi gargaɗin cewa ɗaura wa jama’a ’yan takara ka iya tarwatsa jam’iyyar
  • Kente ya yi wannan gargaɗi ne a garinsu na Wukari ranar Laraba bayan ya yi nasarar miƙa fom ɗin takararsa tare da tsallake tantancewar da aka yi
  • A bayanan da ya yi, ya ce ya shiga takarar ne kawai bayan matsin lamba daga jama’a ya yi yawa sosai har ya kasa ci gaba da ƙin amincewa da kiransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a Taraba, David Sabo Kente, ya yi gargaɗin cewa yunƙurin tilastawa jama'a ’yan takara da sunan yarjejeniya ka iya jefa jam’iyyar cikin rikici.

Kara karanta wannan

2027: Yadda 'yar Kwankwaso ta shawo kan shi game da hada kai da Obi

Rahotanni sun nuna cewa Kente ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a garinsu na Wukari ranar Laraba.

Mai neman takara a APC a Taraba, David Sabo Kente
Lokacin da David Sabo Kente ya isa Wukari. Hoto: Abdulmumin Iman
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ya jaddada cewa zaɓen fidda gwani na gaskiya da adalci ne kaɗai hanyar da za ta samar da amintattun ’yan takara na kujerar gwamna, sanata da kuma majalisar wakilai a jihar.

APC ta tantance Sabo Kente

Jigon na APC ya ce ya riga ya miƙa takardun neman takararsa tare da tsallake tantancewar jam’iyyar, yana mai bayyana kansa a shirye tsaf domin shiga zaɓen fidda gwani na gwamna.

The Sun ta wallafa cewa Kente ya nuna ƙwarin gwiwar cewa zai yi nasara a zaɓen, yana mai cewa bai tsoron gogayya da kowa.

“Me zai sa wani ya nace sai an yi yarjejeniya? Ni ba na tsoron zaɓen fidda gwani domin ina da goyon baya daga mafi yawan ’yan APC a faɗin jihar,”

In ji Kente.

Gwamna Agbu Kefas
Agbu Kefas yayin wani taro a Jalingo. Hoto: Taraba State Government
Source: Facebook

Dalilin shigar takarar Kente

A cewar David Sabo Kente, matsin lamba daga magoya baya da masu ruwa da tsaki a faɗin jihar ne ya sa ya shiga takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Abin da zai faru a jam'iyyar APC idan aka gaza samun ɗan takara ta hanyar sulhu

“Matsin lamba ta yi yawa har na kasa ci gaba da ƙin amincewa.
"Makonni kaɗan da suka gabata, shugabanni da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 16 na jihar sun taru a Wukari inda suka yanke shawarar amfani da kuɗinsu domin sayo min fom ɗin takara domin ceto Taraba a 2027,”

Kente ya kuma yi kira ga al’ummar Kudancin Taraba da ’yan Najeriya gaba ɗaya su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya samu wa’adi na biyu a 2027.

An goyi bayan Pantami a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode ya nuna goyon baya ga Sheikh Isa Ali Pantami.

Fani-Kayode ya yi maganar ne yayin da ake cigaba da shirin zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC domin samar da dan takarar gwamna a Gombe.

Pantami da Sanata Saidu Alkali sun ki amincewa da dan takarar da gwamnan Gombe ya nuna, inda suka bukaci a yi zaben fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng