'Yadda 'Yan Arewa za Su Zabi Tinubu a 2027,' Uba Sani Ya Fito da Bayanai

'Yadda 'Yan Arewa za Su Zabi Tinubu a 2027,' Uba Sani Ya Fito da Bayanai

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi magana kan yadda 'yan Arewacin Najeriya za su zabi shugaba Bola Tinubu a 2027 duk da korafin da ake yi
  • Uba Sani ya yi karin haske kan maganar fitar da 'yan takara a APC domin zaben 2027 da kuma rikici kan shugaban gwamnonin jam'iyyar
  • Gwamnan Kaduna ya yi maganganun ne yayin da 'yan siyasa ke cigaba da shirye-shiryen da suka hada da sayen fom da sau din takara da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa ’yan Najeriya, musamman 'yan Arewa, za su zaɓi shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu a zaben 2027.

Ya bayyana haka ne yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ke cigaba da fafutukar ganin ya samu nasarar lashe zabe karo na biyu a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Da hannun Tinubu": ADC ta yi fallasa kan 'dalilin' farfado da jam'iyyar NDC

Gwamna Uba Sani da shugaba Bola Tinubu
Uba Sani yayin ganawa da Bola Tinubu a Aso Rock Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Uba Sani: 'Za a zabi Tinubu a Arewa'

Da yake magana a matsayin baƙo a shirin Politics Today na tashar Channels Television ranar Litinin, gwamna Uba Sani ya ce Tinubu ya samu nasarar daidaita tattalin arziƙin Najeriya tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Gwamnan ya kalubalanci ’yan adawa, waɗanda ke yawan sukar shugaban ƙasa, a kan sauyin da za su iya kawowa, yana mai cewa har yanzu ba su gabatar da wata mafita mai gamsarwa ba.

Game da sake zaben Tinubu a Arewa, ya ce:

“Za su zaɓe shi saboda dalilai biyu. Shin yawancin mutanen da ke adawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu sun taɓa zuwa tashar ku sun ce wannan ne mafitar da muke da ita a kan ilimi ko lafiya ko noma?

Maganar tantance 'yan takarar APC

Gabanin babban zaɓen 2027, jam’iyyar APC ta fuskanci koke-koke daga wasu masu neman takara kan tsarin cimma matsaya, lamarin da ya janyo fargabar yiwuwar rikici a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

An yaye daga ADC, 'yan majalisa 17 sun bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Sai dai gwamna Uba Sani ya ce lamarin ba mai tayar da hankali ba ne:

“Gaskiyar magana, wannan yanayin ba abin damuwa ba ne, saboda bari in ba da misali daga jihata. Tabbas, na kira masu neman takara, kuma muka amince cewa inda za mu iya yin matsaya, mu yi, amma inda mutane ba su amince da matsayar ba, dokar zaɓe ta fadi mafita karara."

Kan rahotannin da ke cewa akwai saɓani a cikin ƙungiyar gwamnonin APC, gwamna Uba Sani, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Hope Uzodimma ya ce babu wata babbar matsala.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamna Uba Sani a ofis a Kaduna. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

David Offor ya wallafa bayanin da Uba Sani ya yi a shafinsa na X:

Aregbe bai koma APC ba

A wani labarin, mun kawo muku cewa sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa bai koma APC mai mulki ba.

Ya bayyana cewa suna shirye-shiryen kifar da gwamnatin Bola Tinubu da jam'iyyar APC a zaben 2027 saboda yadda suke hada kan jama'a.

Aregbesola ya kaddamar da dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a jihar Osun yayin taron da suka yi yana mai cewa shi ne zai yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng