Kano da Wasu Jihohin Arewa 4 da Zaben Gwamna Zai Dauki Hankali a 2027
Yayin da zaben 2027 ke kara kusantowa, gwamnonin da za su kammala wa'adi na farko sun fara shirye-shiryen neman tazarce domin yin zango biyu kamar yadda dokar Najeriya ta tanada.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sai dai wasu gwamnonin na fuskantar kalubale mai girma a kokarinsu na neman wa'adi na biyu saboda bata wa da iyayen gidansu da kuma wasu malamai da suka shigo siyasa.

Source: Facebook
Gwamna Abba zai fuskanci kalubale a 2027
Kano na daya daga cikin wadannan jihohi da za su fi daukar hankali sakamakon rabuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf da uban gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yayin da Gwamna Abba ya koma APC kuma yake shirin neman tazarce a 2027, madugun Kwankwasiyya ya hade da manyan 'yan adawa a ADC domin karbe mulkin Kano a zabe mai zuwa.
Jihohi 5 da zaben su zai dauki hankali
Irin wadannan kalubale da wasu dalilai ne suka sanya zaben gwamnan Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya za su dauki hankali matuka, kuma za a zuba ido aka abin da zai faru a 2027.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jihohin da ake hasashen za su dauki hankalin Najeriya a zaben gwamnonin da za a yi ranar 6 ga watan Fabrairun 2027.
1. Jihar Kano
Kano ita ce a sahun farko a jihohin Arewa da ake ganin zabeen gwamna da za a yi a 2027 zai yi zafi kuma zai dauki hankali matuka.
A zaben 2023, Gwamna Abba Kabir Yusur na NNPP, wanda ke tare da Kwankwaso a lokacin, ya kayar da dan takarar jam'iyya mai mulki, APC, Dr. Nasir Yusuf Gawuna.
Sai dai a yanzu, Abba ya bar gidan Kwankwaso, ya koma tsagin tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, yayin da Gawuna ya koma tafiyar Kwankwasiyya, cewar rahoton Guardian.

Source: Facebook
Bisa wannan sauye-sauye da aka samu, ana ganin zaben gwamnan Kano na 2027 zai dauki hankali matuka saboda yadda Gwamna Abba zai kara da dan takarar da Kwankwaso zai marawa baya.
2. Jihar Kaduna
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani na daya daga cikin gwamnonin Arewa da ake ganin za su fuskanci kalubale wajen neman tazarce a zaben 2027.
Rahoton The Nation ya nuna cewa hakan yana da nasaba da raba gari da gwamnan ya yi da uban gidansa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
El-Rufai ya hada kai da manyan jagororin adawar Najeriya kamar Atiku Abubakar da Peter Obi, domin kalubalantar gwamnatin APC a zaben 2027.
Duk da ADC na fama da rikicin cikin gida, amma ana ganin zaben Kaduna zai dauki hankali fiye da yadda ya faru a 2023 saboda rabuwar Gwamna Uba Sani da El-Rufai.

Source: Facebook
3. Jihar Gombe
Tuni siyasar jihar Gombe ta fara daukar hankali a Arewacin Najeriya bayan babban malamin addinin musulunci kuma tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya nuna sha'awar takara.
Takarar da Isa Pantami ke shirin fitowa a inuwar APC ta ja hankalin yan Arewa, musamman ganin cewa ba a saba ganin manyan malamai kamarsa suna neman kujerar mulki ta gwamna ba.
Duk da dai har yanzu APC ba ta yanke wanda za ta ba tikitin takarar gwamnan Gombe a 2027 ba, mutane sun zuba ido su ga yadda za ta kaya a zabe mai zuwa a jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito Pantami na cewa ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake kan muƙamin gwamnati su ne za su ba da shaidar cancantarsa a zaɓen 2027.

Source: Twitter
4. Jihar Sakkwato
Wani abu da ya kara jan hankalin mutane a siyasar Arewacin Najeriya, shi ne ayyana fitowa takarar gwamnan da Sheikh Bashir Sani Sokoto ya yi.
Malamin Musulunci ya bayyana haka ne a wani wa'azi da ya gabatar, wanda Taskar Malaman Sunnah TV ta wallafa a shafin YouTube.
Wannan lamari ya girgiza siyasar jihar Sakkwato, kuma malamin wanda ake ganin yana da mabiya da yawa, zai fafata da gwamna mai ci, Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC.

Source: Facebook
A daya bangaren kuma, jam'iyyar ADC da ake tunanin malamin zai shiga, karkashin jagorancin Sanata Aminu Waziri Tambuwal, na shirye-shiryen ganin ta karbe mulkin Sakkwato a 2027.
5. Jihar Zamfara
Sauya shekar Gwamna Dauda Lawal daga PDP zuwa APC da fitowa takarar malamin addinin musulunci, Sheikh Abdulmutallib Gusau, sun sa siyasar jihar Zamfara ta fara daukar hankali a wannan karon.
Gwamnan ya koma APC tare da hadewa da Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, wanda har yanzu yana da damar sake neman takarar gwamna kamar yadda doka ta tanada.
A rahoton jaridar Guardian, malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdulmutallib Gusau, ya shiga cikin sahun mutanen da ke son fafatawa da Gwamna Dauda Lawal a zaben 2027.

Source: Facebook
Sheikh Abdulmutallib ya ce matakin da ya ɗauka na shiga siyasa duk da matsayinsa na malamin addini, ya biyo bayan yadda abubuwa ba sa tafiya daidai a ƙasar nan.
Sakamakon haka, ana ganin zaben Zamfara zai dauki hankali duba da manyan jiga-jigan da za su iya neman tikitin APC da kuma takarar shehin, wanda tuni ya shiga ADC.
Da gaske an hana Pantami takara a Gombe?
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya nemi ya hakura da takarar gwamna a Gombe.
An yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci Farfesa Pantami da ya hakura da batun yin takara a zaben 2027.
Sai dai, Farfesan ya fito ya ƙaryata wannan labari gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




