INEC Ta Cire Sunayen Ƴan Takara, an Cire Sunan Jonathan, Goje da Manyan Ƴan Siyasa

INEC Ta Cire Sunayen Ƴan Takara, an Cire Sunan Jonathan, Goje da Manyan Ƴan Siyasa

  • Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar zaɓen 2027 na ƙarshe, inda aka rasa sunan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan
  • Fitattun sanatoci a Najeriya sun rasa sunayensu a cikin jerin takardun ƙarshe da INEC ta fitar wanda ke kara tabbatar da cewa sun damar tsayawa takara a 2027
  • Duk da APC ta mayar da sanatoci shida bayan duba ƙorafe-ƙorafe, wasu fitattun 'yan siyasa sun ci gaba da kasancewa a wajen jerin sunayen ƙarshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na 'yan takarar zaɓen gama gari na shekarar 2027, wanda ya kawo ƙarshen dogon jiran da aka yi.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya ce ya miƙa sunansa ga INEC a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, bai bayyana ba.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Tinubu da Obi suka ki dora wasu muhimman takardunsu a shafin INEC

INEC ta cire sunan Jonathan, Goje da manyan yan siyasa
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

INEC: Sanatocin da aka cire sunayensu

Haka kuma, sanatocin Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa, Garba Maidoki na Kebbi ta Kudu, da tsohon gwamnan Gombe Danjuma Goje sun rasa gurbi, cewar Punch.

Rahoton ya zo ne watanni biyu bayan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tabbatar wa sanatocin da suka rasa tikitin APC cewa shugabannin jam'iyyar na duba ƙorafensu.

Sai dai bincike ya nuna cewa duk da APC ta mayar da sanatoci shida bayan nazarin ƙorafe-ƙorafe, wasu manyan 'yan siyasa ba su shiga jerin ƙarshe ba.

A Delta, sunan Ned Nwoko bai bayyana a jerin INEC da aka rataya a Asaba ba, yayin da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa ya zama ɗan takarar sanata na jam'iyyar.

Hakan ya tabbatar da cewa Nwoko ya sha kaye tun a zaɓen fidda gwani na APC, kamar yadda aka bayyana a baya.

An cire sunan Goje daga cikin masu neman takara
Sanatan Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje. Hoto: Muhammad Adamu Yayari.
Source: Facebook

Sanatocin da INEC ta fitar da sunayensu

A Gombe kuma, tsohon gwamna Danjuma Goje ya rasa tikitin APC bayan Mohammed Ahmed mai ritaya daga aikin 'yan sanda ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Komai ya fito fili, INEC ta saki bayanan karatun Tinubu da Shettima

A ɓangaren PDP, tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya zama ɗan takarar sanatan Gombe ta Arewa, yayin da Anthony Siyako ya samu tikitin Gombe ta Kudu.

A Bauchi, sanatansa Shehu Buba da ɗan Majalisar Wakilai Mansur Soro ba su bayyana a jerin ƙarshe na INEC ba, cewar Vanguard.

An bayyana cewa Shehu Buba ya koma jam'iyyar PRP inda ya samu tikitin takarar gwamna, yayin da Mansur Soro ya sanar da cewa ba zai sake neman wata kujera ba.

A watan da ya gabata, kwamitin APC ya soke nasarar wasu 'yan takarar sanatoci tare da mayar da sanatoci shida bisa shawarar kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe.

Jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da Kogi, Benue, Taraba, Ondo, Abia, Niger, Kwara, Kaduna da Ebonyi.

Tsagin PDP ya mika sunan Jonathan

A baya, an ji cewa tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ya ce ya miƙa wa INEC takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Tsagin ya ce ya bi tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 wajen miƙa sunayen da hannu, tare da gargaɗin INEC kada ta wallafa wata daban

PDP ta zargi INEC da nuna son kai, tana mai cewa za ta bi duk hanyoyin shari'a domin hana jam'iyyar daga shiga takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.