An Jefa Tambayoyi Ga Tinubu kan Rashin Takardun Firamare, Sakandare daga INEC

An Jefa Tambayoyi Ga Tinubu kan Rashin Takardun Firamare, Sakandare daga INEC

  • Tsohon minista Solomon Dalung ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya yi bayani kan dalilin rashin mika wasu takardunsa ga INEC
  • Dalung ya ce abin da ya faɗa ba zargi ba ne, illa abin da ya gani a takardun 'yan takarar shugaban ƙasa da INEC ta wallafa
  • Ya ce gaskiya da bayanai dalla-dalla suna ƙarfafa amincewar jama'a, ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya bi ƙa'idoji irin na sauran 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya yi magana game da fitar da takardun Bola Tinubu da INEC ta yi.

Dalung ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa aka bar guraben bayanan karatun firamare da sakandare babu komai.

Dalung ya kalubalanci Tinubu kan takardun makaranta
Shugaba Bola Tinubu da tsohon minista, Solomon Dalung. Hoto: Bayo Onanuga, Barr. Solomon Dalung.
Source: Facebook

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Dalung ya ce ya lura cewa Shugaba Tinubu ya bayyana digirin jami'arsa kawai, yayin da aka bar guraben bayanan makarantun firamare da sakandare babu cikawa.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi ga yan Najeriya game da addininsu

INEC ta fitar da bayanan yan takara

A ranar Asabar ne INEC ta fitar da bayanan sirri da takardun da 'yan takarar shugaban ƙasa suka miƙa domin zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

Hakan ya buɗe damar duba cancantar 'yan takarar kamar yadda doka ta tanada yayin da ake shirin zaben 2027.

Dalung ya ce wannan ba zargi ba ne, illa abin da ya gani kai tsaye daga takardun da INEC ta wallafa.

Sai dai ya ce hakan ya haifar da tambayar da ta dace a ba ta amsa, wato me ya sa aka bar waɗannan gurabe babu komai.

Ya bayyana cewa amincewar jama'a ga shugabanni tana ƙaruwa ne idan ana bayyana gaskiya ba tare da ruɗani ba.

A cewarsa, shugabancin ƙasa yana buƙatar cikakken bayani domin tabbatar da amincewar al'umma.

Dalung ya caccaki Tinubu kan takardun makaranta
Tsohon minista a Najeriya, Solomon Dalung. Hoto: Barr. Solomon Dalung.
Source: UGC

Abin da Dalung ke bukata daga Tinubu

Dalung ya ce gwamnatin Tinubu da magoya bayanta sun sha jaddada muhimmancin bayanan hukuma da rantsuwar kotu, tare da neman sauran 'yan siyasa su yi bayani kan duk wani gibi a takardunsu.

Kara karanta wannan

Komai ya fito fili, INEC ta saki bayanan karatun Tinubu da Shettima

Ya ƙara da cewa abin da yake magana a kai ba wai sunayen makarantun da shugaban ya halarta ba ne, sai dai ƙa'idar bayyana cikakken tarihin ilimi ga jama'a kamar yadda ake buƙata ga sauran 'yan Najeriya.

A ƙarshe, Dalung ya ce hanya mafi sauƙi ta kawar da jita-jita ita ce bayyana gaskiya. Ya ce masu neman amincewar jama'a dole su kasance a shirye su amsa tambayoyin jama'a tare da ƙarfafa amincewa da shugabancinsu.

INEC ta yi fatali da takarar Jonathan

Mun ba ku labarin cewa hukumar INEC ta ce ba ta amince da takarar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da bangaren Kabiru Turaki na PDP ya ce ya mika mata ba.

Bangaren Turaki ya ce ya mika sunayen Jonathan da sauran 'yan takararsa da hannu bayan INEC ta ki ba su lambobin shiga tsarin intanet.

Rikicin shugabanci a PDP ya kara tsananta yayin da bangaren Turaki ke zargin INEC da nuna son kai kan rikicin cikin gida na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.