Malamin Addinin Musulunci Ya Shiga Takarar Gwamnan Zamfara, Ya Zabi Jam'iyya
- Siyasar jihar Zamfara ta fara daukar zafi bayan an samu sabon dan takara da ke neman kujerar gwamna a zaben 2027
- Malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdulmutallib Gusau, ya shiga cikin sahun mutanen da ke son fafatawa da Gwamna Dauda Lawal
- Ya bayyana cewa fito takara ne domin ceto jihar Zamfara daga matsalolin rashin tsaro da zaman kashe wando da ya addabi matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Gusau, jihar Zamfara -Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh AbdulMutallib Mohammad Gusau, ya shiga tseren takarar gwamnan jihar Zamfara.
Sheikh Abdulmutallib Mohammad Gusau ya fito takarar ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC mai adawa.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce malamin addinin Musuluncin ya yi rajista da jam'iyyar ADC a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.
Meyasa malamin ya fito takarar gwamnan Zamfara?
Sheikh Abdulmutallib ya ce matakin da ya ɗauka na shiga siyasa duk da matsayinsa na malamin addini, ya biyo bayan yadda abubuwa ba sa tafiya daidai a ƙasar nan.
Ya koka kan yadda wasu ’yan siyasa ba sa yin imani da ranar sakamako, inda kowa za a yi masa shari’a bisa ga ayyukansa.
“Ni malamin addini ne wanda na shafe lokaci mai tsawo ina yin wa’azi, kuma na yanke shawarar shiga siyasa ne domin in nuna misali na gari, kamar yadda ake cewa ‘aiki ya fi magana,’”
- Sheikh Abdulmutallib Mohammad Gusau
Aliyu Adam Rijau ya sanya bidiyon jawabin malamin a shafinsa na Facebook.
Sheikh Gusau ya koka kan rashin tsaro
Sheikh Gusau, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yanayin rayuwa da tsaro a jihar Zamfara, ya ce babban abin da zai sa a gaba idan aka ba shi dama, shi ne magance ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar, da kuma yaƙi da matsanancin talauci da ya nakasa rayuwar al’umma.
"Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta gaza magance matsalolin tsaro da rashin aikin yi da ke addabar mutanenmu, duk da alƙawarin da ya yi na yaƙin neman zaɓe na cewa zai kawo ƙarshen rashin tsaro cikin watanni uku da shiga ofis.”
“Da yardar Allah, zan sauya wannan yanayin cikin kankanin lokaci idan na zama gwamnan jihar."
"Dole ne in yi iyakacin ƙoƙarina don kawo canji mai kyau a wannan jiha tamu, tare da sanin cewa Allah zai tambaye ni kan shugabancina a gobe ƙiyama.”
“Na daɗe ina wa’azi kan ayyukan saɓo da rashin ɗa’a. Don haka, ba zan bar irin hakan ya faru a ƙarƙashin kulawata ba idan na kasance shugaba."
- Sheikh Abdulmutallib Mohammad Gusau

Source: Facebook
Ya bukaci magoya baya su shiga ADC
Sheikh Gusau, wanda ya yi jawabi ga dubban magoya bayansa jim kaɗan bayan kammala rajista, ya nuna kyakkyawan fata cewa ADC ita ce kaɗai za ta iya kawo canji mai kyau a Najeriya, la’akari da mawuyacin halin tattalin arziƙi da al’umma ke ciki.
Saboda haka, ya yi kira ga magoya bayansa da su yi rajista da jam’iyyar domin ceto ƙasar nan daga rugujewa baki ɗaya.
Pantami ya yi magana kan ayyukansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya tuna baya kan ayyukan da ya gudanar.
Farfesa Pantami ya bayyana cewa ayyukan da ya yi za su yi masa kamfen a lokacin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Kalamansa na zuwa ne yayin da alamu ke nuna yana da niyyar neman takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


