Gwamna Dauda Ya Gana da Shugaba Tinubu, an Ji Abin da Suka Tattauna
- Gwamnan Zamfara ya gana da Mai girma Bola Tinubu bayan kammala taron da shugaban kasa ya yi da gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Shugaban kasar na Najeriya ya samu bayani daga bakin Gwamna Dauda kan halin da ake ciki ta fuskar tsaro da tattalin arziki a jihar Zamfara
- Mai girma Bola Tinubu ya jaddada kudurinsa na ci gaba da ba da dukkanin goyon baya ga jihar Zamfara domin magance matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.
Gwamna Dauda ya gana da Shugaba Tinubu ne domin yi masa bayani kan yanayin tsaro, tattalin arziki, da kuma siyasar jihar Zamfara.

Source: Facebook
Mai magana da yawun bakin gwamnan na Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.
Gwamna Dauda ya tattauna da Bola Tinubu
Suleiman Bala Idris ya bayyana cewa shugaban kasar ya sake jaddada kudurin gwamnatin tarayya na ƙara yawan dakarun sojoji da kuma ba da goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.
Ya ce Gwamna Dauda ya gana da Tinubu ne jim kaɗan bayan shugaban kasar ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Hakazalika, Suleiman ya bayyana cewa Gwamna Dauda ya sanar da Shugaba Tinubu ci gaban da aka samu a Zamfara.
Me Shugaban kasa da gwamnan suka tattauna?
“Babban abin da aka mayar da hankali a kai yayin taron shi ne yanayin tsaro a Zamfara, musamman nuna nasarorin da aka samu zuwa yanzu da kuma gano wuraren da ke buƙatar ingantawa domin sauƙaƙa dawo da zaman lafiya a faɗin jihar."
“Shugaban kasa ya jaddada kudurinsa na ba da cikakken goyon baya ga gwamnatin jihar Zamfara, ciki har da tura ƙarin dakarun sojoji da kayan aiki masu muhimmanci domin tabbatar da gudanar da ayyuka cikin nasara."

Kara karanta wannan
Sanatoci sun gana da Tinubu, an ruwaito cewa ya yi fatali da bukatarsu kan zaɓen 2027
“Bugu da ƙari, Gwamna Dauda ya yi wa Shugaban kasa bayani kan haɓakar tattalin arzikin Zamfara, musamman ƙaruwar kudaden shiga na cikin gida, sannan ya tattauna hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta ƙara ba da goyon baya."
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da kudurinsa na ci gaba da ba da tallafi, wanda ya haɗa da amfani albarkatun tarayya da shirye-shiryen da za a iya amfani da su wajen haɓaka masana’antun cikin gida da samar da damar ayyukan yi a Zamfara.”
- Suleiman Bala Idris

Source: Facebook
Shugaba Tinubu na son sake kinkimo bashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasika ga majalisar dattawa kan bukatar sake ciyo bashi daga kasar waje.
Mai girma Bola Tinubu ya nemi izinin Majalisar Dattawa domin sake ciyo bashin Dala miliyan 516.3 daga bankin Deutschk da ke kasar Jamus.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kinkimo sabon rancen ne domin gina babban titin hanyar Sokoto zuwa Badagry wanda aka fara aikinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
