Bayan Mako 1, 'Yan Bindiga Sun Dauki Sabon Mataki kan Alkalin Kebbi da Suka Sace
- An sako alkalin Babbar Kotun Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, bayan ya shafe mako guda a hannun 'yan bindiga
- Iyalansa sun tabbatar da dawowarsa gida lafiya, inda suka gode wa Allah da kuma duk waɗanda suka yi addu'a da nuna goyon baya
- Har yanzu hukumomin shari'a da jami'an tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan yadda aka kuɓutar da alkalin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kebbi - An sako alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, wanda aka sace mako guda da ya gabata, inda ya koma gidansa lafiya ya kuma haɗu da iyalansa.
Wani ɗan uwansa ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, yana mai cewa alkalin ya dawo gida sa'o'i kaɗan bayan samun 'yancinsa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Source: UGC
An sako alkalin kotun Kebbi
A cewar ɗan uwan, iyalan alkalin sun cika da farin ciki da godiya ga Allah bisa dawowarsa lafiya bayan shafe mako guda a hannun 'yan bindiga, in ji rahoton Vanguard.
Ya ce sun gode wa ma'aikatan shari'a na jihar Kebbi, jami'an tsaro da al'ummar jihar bisa addu'o'i, saƙonnin ta'aziyya da goyon bayan da suka ba su a lokacin wannan ƙalubale.
Ya ƙara da cewa wannan goyon baya ne ya ba iyalan ƙarfin gwiwar jure halin da suka shiga.
Sai dai ya bayyana cewa za a sanar da cikakken bayani kan yadda aka kuɓutar da alkalin a wani lokaci na gaba.
Hukumomi ba su yi magana ba
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin shari'a ta jihar Kebbi da jami'an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan sakin Mai shari'a Bunza ba.
TVC News ta ruwaito cewa sace alkalin ya jawo hankalin jama'a a makon da ya gabata, inda mazauna jihar da masu ruwa da tsaki suka yi kira da a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
Yadda aka sace alkalin
Rahotanni sun ce an sace Mai shari'a Faruku Bunza ne daga gidansa da ke ƙaramar hukumar Bunza da tsakar daren Lahadi, jim kaɗan bayan dawowarsa daga wata tafiya zuwa jihar Sokoto.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar, Umar Hadejia, ya tura jami'an musamman da na tattara bayanan sirri domin ceto alkalin.

Source: Original
Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan wasu 'yan bindiga sun sace shugaban wata ƙaramar hukuma a jihar Zamfara, abin da ya ƙara nuna yadda hare-haren masu garkuwa da mutane ke ƙaruwa a yankin Arewa maso Yamma.
A baya-bayan nan, masu garkuwa da mutane sun fi mayar da hankali kan manyan jami'an gwamnati, alkalai, sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma malamai a jihohin Kebbi, Zamfara, Sokoto da Katsina.
Asali: Legit.ng

