Kotu Ta Ɗauki Mataki kan Buƙatar Belin El Rufai, Malam Zai Zauna a hannun ICPC

Kotu Ta Ɗauki Mataki kan Buƙatar Belin El Rufai, Malam Zai Zauna a hannun ICPC

  • Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ɗage yanke hukunci kan bukatar bada belin Malam Nasir El-Rufai har zuwa makon farko na watan Yuni, 2026
  • Tsohon gwamnan yana fuskantar tuhume-tuhume guda tara da suka haɗa da zargin zamba da kuma cin zarafin ofis wanda ICPC ta shigar
  • Lauyan El-Rufai ya soki wannan jinkiri na kotun, inda ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na siyasa domin tsawaita tsare Malam

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna – Mai shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya ɗage zaman sauraron bukatar belin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, zuwa makon farko na watan Yuni, 2026.

Wannan mataki ya zo ne a zaman kotun na yau Talata, 21 ga watan Afrilu, wanda aka sa ran kotun za ta bayyana matsayarta kan belin tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

Babbar magana: El Rufai ya fallasa sabuwar makarkashiyar da ake kulla masa

Kotu ta dage sauraron bukatar belin El-Rufai, zai ci gaba da zama a hannun EFCC.
Malam Nasir El-Rufai na fitowa daga motar hukumar ICPC da aka isa kotu a Kaduna. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Kotu ta dage zaman belin Nasir El Rufai

Hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda tara, in ji rahoton Daily Trust.

Waɗannan zarge-zarge sun hada da batutuwan da suka shafi zambar kuɗaɗe da kuma yin amfani da iko ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da yake kan karagar mulki a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

A zaman kotun na ranar Talatar da ta gabata, alkalin ya saurari hujjojin lauyoyin tsohon gwamnan na neman belinsa, inda aka tsara yanke hukunci a yau.

Sai dai, tun da an ɗage zaman zuwa watan Yuni, El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a hannun hukumar ICPC.

Zaman El Rufai a ICPC bayan hukuncin kotu

Idan za a iya tunawa, tsohon gwamnan ya sami nasarar samun beli a wata shari’ar daban da ke gaban wata Babbar Kotun Tarayya a Kaduna.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027

A waccan shari’ar, Mai shari’a Rilwanu Aikawa ya ba El-Rufai belin Naira miliyan 200, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Daga cikin sharuɗɗan belin har da hana shi yin hira da 'yan jarida game da shari’ar, sannan kuma dole ne ya rinka halartar dukkan zaman kotu.

Sai dai, duk da wancan belin, wannan shari’ar ta ICPC da ke gaban Mai shari’a Darius Khobo ita ce ta zama silar ci gaba da tsare shi yanzu.

Malam Nasir El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun EFCC har zuwa Yuni.
Malam Nasir El-Rufai a lokacin da ya isa harabar babbar kotun Kaduna tare da jami'an ICPC. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

"Akwai siyasa a ciki," Lauyan El-Rufai

Bayan kammala zaman kotun na yau, lauyan tsohon gwamnan, Ukpon Akpan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka ɗage shari’ar zuwa wani lokaci mai tsawo.

Akpan ya bayyana cewa wannan jinkirin ba komai ba ne face "manufar siyasa" da aka shirya domin takura wa Malam Nasir El-Rufai.

A halin yanzu, El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a tsare a hannun hukumar ICPC har sai an cika sharuɗɗan belin da kotun tarayya ta gindaya, kuma har sai lokacin da wannan sabuwar shari’ar ta sake dawowa gaban kotu a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa

'Ana kulla mun makarkashiya,' El-Rufai

A wani labari, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufai, ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin wani sabon kulle-kulle na sanya shi cikin ayyukan laifi.

Tsohon gwamnan jihar na Kaduna, ya yi zargin cewa akwai wani tsari na hadin gwiwa da nufin bata masa suna da kuma tsawaita tsare shi.

El-Rufai ya tuna da wani lamari da ya faru a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, lokacin da aka yi yunkurin kama shi bayan isowarsa filin jirgin sama na Abuja daga birnin Cairo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com