Gwamna Inuwa Ya Bukaci Pantami Ya Hakura da Takara a 2027? Magana Ta Fito

Gwamna Inuwa Ya Bukaci Pantami Ya Hakura da Takara a 2027? Magana Ta Fito

  • Tsohon Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, na da burin tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe karkashin inuwar jam'iyyar APC
  • An yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci Farfesa Pantami da ya hakura da batun yin takara a zaben 2027
  • Tsohon Ministan ya fito ya yi magana kan gaskiya ko rashin gaskiyar rahotannin da aka yada kan batun takararsa ta gwamna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - An yada wasu rahotanni kan batun takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a zaben gwamnan jihar Gombe na 2027.

Rahotannin sun nuna cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci Farfesa Pantami da ya hakura da yin takara.

An yada rahotanni kan takarar Pantami a 2027
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe da Farfasa Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: Ismaila Uba Misilli, Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Wani mai suna @TheoAbuAgada a shafin X ya kawo batun ba Pantami hakuri kan yin takara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," Malaman Musulunci sun tunkari gwamna kan 'tsarin' da ya kawo a Najeriya

An yada jita-jita kan takarar Isa Pantami

A cewarsa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bukaci Farfesa Pantami da ya janye daga batun yin takara.

Ya kara da cewa gwamnan ya bukaci tsohon Ministan sadarwar a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari da ya goyi bayan dan takarar da jam'iyyar APC ta amince da shi.

Hakazalika, ya nuna cewa Pantami bai ji dadin abin da gwamnan ya yi masa ba na ya hakura da yin takara.

"Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya buƙaci Farfesa Isa Ali Pantami da ya janye sha'awar takarar gwamna, sannan ya goyi bayan ɗan takarar da jam'iyyar APC ta amince da shi yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a daren ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Gombe."
"Majiyoyi sun nuna cewa Pantami bai ji daɗin wannan hukunci ba."

- Theo Abu Agada

Wane martani Farfesa Pantami ya yi?

Sai dai, Farfesa Pantami ya fito ya ƙaryata wannan labari gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa.

Kara karanta wannan

Malamin addinin Musulunci ya shiga takarar gwamnan Zamfara, ya zabi jam'iyya

Farfesa Pantami ya yi martanin ne a wani rubutu a shafinsa na X a ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026.

“Wannan ba gaskiya ba ne. Babu abin da ya faru makamancin haka. Gwamnan bai buƙaci kowa da ya janye sha’awarsa ta takara ba. Hasalima, Gwamnan ya ba ni wata karramawa ta musamman ta hanyar gayyata ta na kasance ɗaya daga cikin masu jawabi a wurin taron.”

- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami

Pantami ya musanta karyar da aka yada a kansa
Farfesa Pantami yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da littafi kan ayyukansa Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Ya ci gaba da mayar da martani ga wanda ya yaɗa labarin (Theo Abu Agada) da cewa:

“Ka sani ba za ka taɓa samun nasara da mugun nufinka ba. Idan Allah yana tare da kai, babu wani mummunan shiri da zai yi nasara a kanka.”

Pantami ya kare kansa kan kalaman siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya kare kansa kan batun ya taba cewa kada malamai su shiga siyasa.

Farfesa Isa Pantami wanda shi kan shi masanin addinin musulunci ne ya bayyana cewa bai taba haramtawa malamai shiga a dama da su cikin harkokin siyasa ba.

Pantami ya bayyana cewa batun hana shiga siyasa bai taba fitowa daga bakinsa, ya kuma kalubalanci duk wanda yake da hujja to ya nuna masa ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng