Jerin Mutanen da Pantami zai Gwabza da Su a Neman Tikitin Gwamnan APC a Gombe

Jerin Mutanen da Pantami zai Gwabza da Su a Neman Tikitin Gwamnan APC a Gombe

Sheikh Isa Ali Pantami zai fafata da manyan 'yan siyasa, ma'aikata da 'yan kwangila wajen neman tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC a Gombe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Masu sha'awar tsayawa takarar gwamna a Gombe na cigaba da nuna alamun za a dama da su yayin da zaben 2027 ke kara karatowa.

Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami na cikin fitattun mutanen da suka nuna alamun za a fafata da su a neman tikitin takara a jam'iyyar APC.

Yan takarar APC a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya yayin zama da masu son takara a APC a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku jerin gogaggun 'yan siyasa kamar Jamilu Isiyaku Gwamna da Sheikh Isa Pantami zai fafata da su.

Jam'iyyar APC za ta tsaida 'yan takara ne ta hanyar zaben kato bayan kato ko kuma a samu maslaha idan masu neman tikiti za su yi ijima'i.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya shiga gaba, zai jagoranci 'yan adawa karfafa yaki da APC, Tinubu

Isa Ali Pantami bai taba tsayawa takara ba, amma wannan karo tsohon minista ya nuna alamar zai so ya muki Gombe a inuwar APC.

Masu neman tikitin gwamnan APC a Gombe

1. Jamilu Isiyaku Gwamna

Jamilu Isiyaku Gwamna gogaggen dan siyasa ne da ya shafe shekaru yana neman zama gwamnan jihar Gombe a jam'iyyu daban-daban.

Gwamna ya yi takara tare da tsofaffin gwamnonin jihar Gombe da suka hada da Muhammadu Danjuma Goje da marigayi Abubakar Habu Hashidu.

Jamili Isiyaku Gwamna
Jamilu Isiyaku Gwamna a taron APC a Gombe. Hoto: Abdul Fatah
Source: Facebook

A yanzu haka, Punch ta wallafa cewa Jamilu ya ayyana cewa zai nemi takarar gwamna a APC, inda ake ganin za su fafata da Pantami.

2. Saidu Ahmed Alkali

Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya yi murabus daga matsayin ministan sufuri domin shiga neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a APC.

Sa'idu Alkali da ake kira da Dan Alkali ya kasance daya da cikin 'yan siyasar jihar Gombe da suka wakilci Gombe ta Arewa a majalisar dattawa.

Inuwa Yahaya da Saidu Ahmed Alkali
Inuwa Yahaya na magana da Saidu Ahmed Alkali a wajen taro. Hoto: Saidu Ahmed Alkali
Source: Facebook

A yanzu haka, Dan Alkali da ya fito daga karamar hukumar Dukku, zai kasance cikin wadanda za su fafata da Pantami a neman tikitin takarar gwamna a Gombe.

Kara karanta wannan

Kamar Buhari, an fara tarawa Pantami miliyoyin kudin fom din takara

3. Usman Bello Kumo

Usman Bello Kumo na cikin 'yan fitattun 'yan siyasa a Gombe, musamman a karamar hukumar Akko da yake cikin jerin masu neman gwamna a APC a 2027.

Tribune ta wallafa cewa Usman Bello ya halarci wani taro da gwamna Inuwa Yahaya ya yi da masu sha'awar tsayawa takara a jihar.

Usman Bello Kumo
Usman Bello Kuma a hagu na gaisawa da Jamilu Gwamna a tsakiya da Salihu Baba Alkali. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Source: Facebook

Kasancewar ya wakilci karamar hukumar Akko majalisar wakilai bayan rike mukamin shugaban karamar hukumar a baya, kuma yana shiri da gwaman jihar, ana gain zai taka rawa sosai a zaben fitar da gwani.

4. Alhaji Yunusa Yakubu

Alhaji Yunusa Yakubu ƙwararren ɗan kasuwa ne kuma gogaggen a harkar gine-gine, ya nuna ƙwarewa wajen kafa kamfanin Lubell.

Ya shiga aikin gwamnati a karon farko a shekarar 1987 a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Bauchi, bayan kammala digirinsa na farko da na biyu daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarun 1984 da 1986.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi a Gombe, Sanatan PDP ya koma jam'iyya mai mulki

Duk da cewa ba sananne ba ne sosai a fagen siyasar jihar Gombe, ana ganin zai yi tasiri sosai a neman tikitin takarar gwamna a APC saboda kusancinsa da gwamna Inuwa Yahaya.

Yunusa Yakubu da Jamilu Gwamna
Jamilu Gwamna a dama, Yunusa Yakubu a hagu a wajen taron APC na kasa. Hoto: Arc. Yunusa Yakubu, FNIA
Source: Facebook

5. Umaru Kwairanga, Sarkin Fulani

Alhaji Umaru Kwairanga tsohon dan siyasa ne kuma da kusan kowa ya sani a jihar Gombe kasancewar ya shafe shekaru yana nuna sha'war takara.

A wannan karon ma, Umaru Kwairanga da ke matsayin Sarkin Fulanin Gombe ya nuna alamun za a fatata da shi wajen neman tikitin takarar gwamna a APC a jihar Gombe.

Sarkin Fulanin Gombe, Sheikh Pantami da Aliyu Kombat
Umaru Kwairanga a hagu, Sheikh Pantami a tsakiya da Aliyu Kombat a dama. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

6. Aliyu Muhammad (Kombat)

Aliyu Mohammed wanda aka fi sani da ‘Kombat’ na cikin matasan da suka nuna alamun za su yi takarar gwamna a Gombe a zaben 2027 a kwanakin baya.

Sai dai Daily Trust ta wallafa cewa ya fito ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar kowanne muƙamin siyasa ba a watan Yulin 2025.

Aliyu Mohammed Kombat
Aliyu Mohammed Kombat yayin wani taro a Gombe. Hoto: Aliyu Mohammed
Source: Facebook

Sai dai ganin shi a taron da gwamna Inuwa Yahaya ya yi da 'yan takara ya nuna alamun ya sauya matsayarsa game da batun.

Sauran masu neman samun takara a Gombe

Kara karanta wannan

Za a gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki gaban kotu

Daga cikin wadanda ake hasashen Pantami zai fafata da su akwai manyan mutane masu tasiri kamar kwamishinan kudin jihar, Muhammad Gambo Magaji.

Akanta janar na jihar Gombe, Aminu Umar Yuguda, wadanda ake ganin na kusa da Gwamna Inuwa Yahaya ne na cikin wadanda ake ambatonsu a harkokin siyasar jihar.

Shugabannin APC tare da Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya da shugabannin APC a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Sauran masu neman takarar gwamna a karkashin APC a jihar Gombe sun hada da Abubakar Bappah da kuma Abubakar Sadiq Shua'ibu.

Legit ta tattauna a Umar Bello

Wani mai bibiyar harkokin siyasa a jihar Gombe, Umar Bello ya bayyanawa Legit Hausa cewa a cikin mutanen da suka nuna sha'awar takara kadan ne masu yi da gaske.

Umar ya ce:

"Yawan su ba zai zama cikas ga Pantami ba, domin ba kowa ba ne a cikinsu ya ke da niyya mai karfi a bisa alamu.
"Masu yi da gaske ba su wuce uku zuwa hudu ba, amma dai lokaci zai bayyana komai."

Maganar Gwamna Inuwa kan takarar 2027

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi zama na musamman da masu ruwa da tsaki na APC kan siyasar 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya sauya akalar siyasarsa bayan sanya labule da Peter Obi

Gwamnan ya bukaci a marawa duk wanda ya samu tikitin takarar gwamna a jihar da saura kujerun da jam'iyyar APC za ta tsayar da 'yan takara.

Game da zaben shugaban kasa kuma, Inuwa Yahaya ya yi kira ga jama'a da marawa shugaba Bola Tinubu baya domin komawa mulki karo na biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng