Umahi: Abin da Tinubu Ya Gayawa Ministan da Aka Nemi Ya Kora kan Mutuwar Budurwa a Gidansa
- Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi masa magana bayan an nemi ya kore shi saboda mutuwar wata ma'aikaciya
- David Umahi ya ce wasu sun mayar da mutuwar wata ma’aikaciyarsa, Mary Habila, batun siyasa tare da neman a tsige shi
- Ministan bai yi bayani kan binciken da ake gudanarwa kan mutuwar Habila ba, amma ya ce zai ci gaba da sauke nauyin da ke kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi watsi da kiraye-kirayen a tsige shi daga mukaminsa bayan mutuwar wata ma’aikaciya a gidansa mai suna Mary Habila.
Umahi ya ce maimakon tsige shi, Shugaba Bola Tinubu ya umurce shi da ya ci gaba da mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan raya ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan
Babban darakta a Kannywood Aminu Saira ya yi sabon aure, hotunan matansa sun jawo cece kuce

Source: Facebook
Mutuwar Mary ta jawo cece-kuce
Jaridar The Punch ta ce Ministan ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya fara yaduwa a dandalin X ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026.
Martanin Umahi ya biyo bayan suka da ce-ce-ku-ce da suka taso sakamakon mutuwar Mary Habila, wata ma’aikaciya da ke aiki a ma’aikatar ayyuka ta tarayya.
Mutuwar Habila a watan Yunin shekarar 2026 ta jawo martani mai yawa a shafukan sada zumunta.
Umahi ya yi martani
A cewar ministan, wasu mutane sun yi kokarin mayar da lamarin batun siyasa tare da neman shugaban kasa ya tsige shi daga mukaminsa.
Umahi ya bayyana cewa:
“Iko da karfi ba na shafukan sada zumunta ba ne, na Allah ne.”
Ya kara da cewa:
“Lokacin da mutane suka dauki mutuwar daya daga cikin ma’aikatana suka fara siyasa da ita, suka ce shugaban kasa ya tsige ni, amma shugaban kasa ya ba su mamaki ya ce, ‘Dave, je ka kara gina tituna.’”
Ana ci gaba da bincike
Kalaman Umahi sun zo ne yayin da jama’a ke ci gaba da nuna sha’awa kan sanin yadda Mary Habila ta mutu.
Ministan bai yi bayani kan binciken da ake ci gaba da gudanarwa kan lamarin ba, amma ya jaddada cewa zai ci gaba da sauke nauyin da ke kansa.
Mutuwar ma’aikaciyar ma’aikatar ayyukan ta tarayya ta jawo martani mai yawa a intanet, inda wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suka bukaci a tabbatar da an yi cikakken bayani kan lamarin.
Hukumomi ba su sanar da sakamakon karshe na binciken da ake yi kan yadda Mary Habila ta mutu ba.

Source: UGC
Umahi ya yi magana kan mutuwar Mary Habila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana bayanan tattaunawar ƙarshe tsakanin marigayiya Mary Habila wadda ta mutu a gidansa da saurayinta.
Ministan ya bayyana cewa ta roƙe shi kada ya katse wayar kafin rasuwarta wanda ya zama shi ne kalamanta na karshe.
David Umahi ya ce Mary Habila ta kasance kamar 'yarsa, domin ta rayu tare da iyalansa tsawon shekaru uku, kuma ya san ta sosai.
Asali: Legit.ng
