Girgizar Kasa Ta Tayar da Hankali a Kasar Musulunci Ta Masar
- Wata girgizar kasa mai karfin maki 5.5 zuwa 5.6 ta Richter ta girgiza sassan kasar Masar da sanyin safiyar Litinin, lamarin da ya jefa mutane cikin fargaba
- Gwamnatin Masar ta ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, yayin da aka sanya asibitoci da hukumomin agaji cikin shirin ko-ta-kwana
- Mahukunta sun bayyana cewa cibiyar girgizar na kusa da birnin Suez, kuma ana ci gaba da sanya ido domin tabbatar da lafiyar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Alkahira – Wata girgizar kasa mai karfin maki 5.5 zuwa 5.6 ta Richter ta girgiza sassan kasar Masar da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar Litinin, lamarin da ya sa mutane da dama suka farka cikin firgici.
Bayan afkuwar lamarin, hukumomin kasar sun gaggauta hada dakunan bayar da agajin gaggawa, tare da sanya asibitoci da motocin daukar marasa lafiya cikin shirin ko-ta-kwana.

Source: Getty Images
Egypt Today ta rahoto cewa Cibiyar Binciken Taurari da Ilimin Kasa ta Masar ta ce cibiyar girgizar tana da tazarar kusan kilomita 38 daga birnin Suez, a zurfin kusan kilomita 10.
Bayanin gwamnatin Masar
Ma'aikatar Lafiya ta Masar ta tabbatar da cewa babu rahoton mutuwa ko jikkata sakamakon girgizar kasar a lokacin da ta fitar da sanarwarta.
Hakazalika, kungiyar agajin Red Crescent ta Masar ta ce ba ta samu wani rahoton asarar rayuka ko lalacewar kadarori ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.
An bayyana cewa an ci gaba da sabunta bayanan girgizar ne yayin da na'urorin sa ido daga wurare daban-daban ke tattara karin bayanai.
Halin da mutane suka shiga
Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin Greater Cairo sun ji girgizar ta hanyoyi mabambanta, inda wasu suka ce gadaje, tagogi da fitilu sun rika motsi, yayin da wasu ba su ji komai ba.
Masana sun bayyana cewa yadda mutum zai ji girgizar kasa ya danganta da nisan da yake daga cibiyar girgizar, zurfinta, yanayin kasa, irin ginin da yake ciki da kuma ko yana farke ko barci.
An kuma ce kasancewar girgizar ta faru a zurfin kusan kilomita 10 ne ya sa mutane da dama suka ji ta, duk da cewa ba a samu rahoton wata babbar barna ba.

Source: Getty Images
Malamin addinin Musulunci, Dr Muhammad Salah ya wallafa sako a shafinsa na Facebook yana tabbatar da faruwar girgizar kasar, inda mutane suka rika masu addu'o'i.
An yi girgizar kasa a Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla mutane uku sun jikkata bayan girgizar kasa biyu da suka afku a yankin Kozran na lardin Kermanshah da ke yammacin Iran.
Rahotanni sun ce girgizar farko ta kai maki 5.2 a ma'aunin Richter, yayin da ta biyu ta kai maki 5.7 cikin mintuna biyar kacal.
Hukumomin agajin gaggawa sun tura tawagogin tantance barnar da girgizar ta haddasa zuwa yankin domin duba halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng

