Ministan Makamashi na Shirin Ajiye Aiki, zai Shiga Takarar Gwamna a 2027

Ministan Makamashi na Shirin Ajiye Aiki, zai Shiga Takarar Gwamna a 2027

  • Ana hasashen cewa ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu zai ajiye mukaminsa domin shiga neman takarar gwamna a zaben 2027
  • Hakan na zuwa ne bayan Adelabu ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa, inda ya mika masa wasu muhimman takardu
  • Ba wannan karon ba ne ministan ya fara neman gwamna, domin an fafata da shi a 2019 a karkashin jam’iyyar APC da kuma zaben a 2023

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Ana hasashen cewa ministan makamashin Najeriya, Adebayo Adelabu, na iya ajiye mukaminsa domin neman takarar gwamna a jihar Oyo.

Hakan na zuwa ne yayin da ministoci da masu rike da mukaman gwamnati ke cigaba da ajiye ayyukansu domin shirin shiga takara a zaben 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Za a gurfanar da ministan Buhari, malamin Musulunci da wasu a kotu

Adebayo Adelabu da Bola Tinubu
Lokacin da Adebayo Adelabu ya ziyarci Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Majiyoyi na kusa da fadar shugaban kasa da kuma ministan sun tabbatar wa Punch cewa Adelabu zai yi murabus ko dai a yau ko kafin karshen mako.

Adelabu ya gana da Tinubu

Batun murabus din na zuwa ne bayan wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026 da aka bai wa masu mukaman siyasa na gwamnatin tarayya su ajiye aiki.

The Cable ta wallafa cewa Bayo Adelabu ya gana da Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata, 21 ga watan Afrilun 2026 domin sanar da shi burinsa na siyasa a jihar Oyo.

An ga ministan a fadar shugaban kasa, amma bai yi magana da manema labarai ba bayan ganawar, lamarin da ya bar jama'a cikin duhu.

Ministan makamashi zai yi murabus

Wani na kusa da shi ya ce Bayo Adelabu zai yi murabus a kwanan nan domin mayar da hankali kan neman gwamna a jihar Oyo.

Ya ce:

“Zai yi murabus, amma ban san ko Laraba ko daga baya cikin makon ba. Amma tabbas zai ajiye mukaminsa.”

Kara karanta wannan

2027: Minista a gwamnatin marigayi Buhari ya ayyana neman takarar gwamna

Ya kara da cewa:

“Ya gana da shugaban kasa kuma ya sanar da shi burinsa. Ya samu amincewar Shugaban kasa. Haka kuma ya yi masa bayani kan ayyukansa cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.”

Adelabu ya gana da 'yan APC

Bayan ganawar, an ce ya gana da tsohon gwamnan jihar Osun kuma jigo a jam’iyyar APC, Adebisi Akande, da kuma tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Pius Akinyelure.

Adebayo Adelabu a wajen taron siyasa a Oyo
Adebayo Adelabu na yi wa jama'a a bayani a taron APC a Ibadan. Hoto: Bayo Adelabu
Source: Facebook

Adelabu, wanda ya tsaya takarar gwamna a 2019 a karkashin jam’iyyar APC da kuma a 2023 karkashin jam’iyyar Accord, bai boye aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2027 karkashin APC ba.

Jam’iyyar APC ta sanya ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaben fidda gwani na gwamna, inda ta kayyade kudin fom din ‘yan takara zuwa Naira miliyan 50.

An zabi mataimakin gwamna a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya zabi Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan da zai yi aiki da shi a Kano.

Kara karanta wannan

A karon farko, matatar Dangote ta hako 'danyen mai a Najeriya

Hakan na zuwa ne bayan murabus da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi bayan Abba ya koma APC.

Yanzu haka dai kallo ya koma kan majalisar dokokin jihar Kano, inda Abba Kabir ya tura sunan Murtala Garo domin a tantance shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng