ArDA Ta Aika Budaddiyar Wasika Dauke da Sunan Malam Adamu ga Shugaba Tinubu
- Kungiyar ArDA ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a gurbin Yusuf Maitama Tuggar
- Ta ce murabus din Tuggar ya bar Bauchi ta Arewa ba tare da wani babban mukami a majalisar zartarwa ta tarayya ba
- Kungiyar ta yi zargin cewa yawancin nade-naden gwamnatin tarayya daga Bauchi sun fi karkata zuwa Bauchi ta Tsakiya da Bauchi ta Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Wata kungiya mai suna Arewa Dignity Advancement Initiative (ArDA) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a matsayin minista.
Kungiyar ta nemi haka ne domin maye gurbin tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, wanda ya yi murabus daga mukaminsa domin beman tikitin takarar gwamnan APC a Bauchi amma bai samu nasara ba.

Source: Twitter
Ana neman Tinubu ya maye gurbin Tuggar
A ruwayar Leaderdhip, shugabar kungiyar ArDA, Hajiya Baheejah Mahmood Abdullahi, ta ce murabus din Tuggar ya bar Bauchi ta Arewa ba tare da babban mukamin zartarwa na gwamnatin tarayya ba.
Hakan dai na kunshe ne A cikin wata budaddiyar wasika da ta aikewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ta bayyana cewa kungiyar ba ta da alaka da wata jam'iyya ko gwamnati, kuma manufarta ita ce tabbatar da adalci, daidaito, shugabanci mai hada kowa da kuma hadin kan kasa.
A cewarta, ArDA ta lura da yadda ake rabon mukaman gwamnatin tarayya, kuma ta damu da yadda Bauchi ta Arewa ke rasa isasshen wakilci.
ArDA ta ja hankalin Tinubu kan adalci
Kungiyar ta yaba da shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu da kokarin gwamnatin wajen ci gaban kasa.
Sai dai ta ce mafi yawan nade-naden gwamnatin tarayya daga Jihar Bauchi sun fi karkata zuwa Bauchi ta Tsakiya da Bauchi ta Kudu.
Ta lissafa mukamai daban-daban da 'yan wadannan yankuna ke rike da su, ciki har da Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, masu ba shugaban kasa shawara da sauran manyan mukaman gwamnati da jam'iyya.
A cewarta, bayan murabus din Tuggar, Bauchi ta Arewa ba ta da wani mukamin zartarwa makamancin haka, in ji rahoton New Telegraph.

Source: Facebook
Ta kara da cewa nada Malam Adamu Adamu zai taimaka wajen gyara abin da ta kira rashin daidaito tare da nuna cewa gwamnatin Tinubu na bin ka'idojin tsarin rabon mukamai, adalci da shugabanci mai hada kowa.
ArDA ta yabawa Adamu Adamu
ArDA ta bayyana tsohon Ministan Ilimin a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari a matsayin gogaggen jami'in gwamnati, dattijo mai kima da kuma jigo mai biyayya ga jam'iyyar APC.
Kungiyar ta ce gogewarsa a aikin gwamnati da kuma karbuwarsa a tsakanin jama'a sun sa ya cancanci a ba shi wannan mukami.
Ta kara da cewa nadinsa zai kara hada kan jama'a, ya bai wa al'ummar Bauchi ta Arewa kwarin gwiwar cewa suna cikin shirin Renewed Hope Agenda, tare da karfafa hadin kan kasa.
Tinubu ya yi sabon nadi a gwamnatinsa
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ɗan tsohon gwamnan jihar Plateau a mukamin hadiminsa na musamman.
Tinubu ya Yakubu Jang, ɗan tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang , a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da naɗin yayin bikin cika shekaru 80 da ƙaddamar da littafin tarihin Jonah Jang a Jos.
Asali: Legit.ng


