Murtala Garo: Abubuwan Sani game da Mai Iya Zama Sabon Mataimakin Gwamnan Kano
Kano – A wani mataki na ba-zata wanda ya girgiza fagen siyasar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin Hon. Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wannan mataki ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon mataimakin gwamnan, Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi tun a ranar 27 ga Maris, 2026.

Source: Facebook
Kiraye kirayen nada Murtala Sule Garo
Tun bayan da Kwamared Gwarzo ya yi murabus, sunan Murtala Garo ya rika karade lungu da sakon Kano, ana ganin shi ne ya fi dacewa da kujerar mataimakin gwamna, in ji rahoton Premium Times.
A lokacin, har wasu shugabannin jam'iyyar APC, karkashin jagorancin tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa suka nemi Gwamna Abba Yusuf, ya ba Garo wannan matsayi.
"Garo shi ne wanda ya fi cancanta da wannan kujera. Ya kasance mutum mai hakuri, biyayya, aiki tukuru. Irinsa ya kamata gwamna ya ja a jiki, musamman a irin wannan lokaci da ake tunkarar babban zabe."
- Alhassan Ado Doguwa.
Za a iya cewa, Gwamna Abba Yusuf ya ji dukkan kiraye-kirayen da ake yi masa, domin kuwa, a ranar 22 ga Afrilu, 2026, aka tashi da labarin cewa an nada Murtala Garo matsayin sabon mataimakin gwamnan Kano.
Abubuwan sani game da Murtala Garo
Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da Garo:
1. Tarihin rayuwa da karatu
Rahoton Independent Post ya nuna cewa an haifi Murtala Sule Garo a ranar 16 ga watan Mayu, 1978, a garin Garo da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano.
Ya fara karatunsa ne a kwalejin kimiyya ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi, sannan ya sami digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Bayero ta Kano (BUK) a shekarar 2012.
2. Gogewar siyasa da muƙaman da ya riƙe
Murtala Garo ya shafe kusan shekaru 20 yana fafatawa a fagen siyasa da shugabanci, inda ya riƙe muƙamai daban-daban da suka haɗa da:
- Mataimaki na musamman ga shugaban ƙaramar hukumar Kabo.
- Sakataren shirye-shirye na kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar APC a Kano.
- Zama zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Kabo.
- Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa (ALGON) reshen jihar Kano.
- Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu a zamanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
- Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
3. Murtala Garo a matsayin 'kwamanda'
Masu fashin baƙi na bayyana Garo a matsayin "Injiniyan Siyasa" wanda ke da karfin juya ra'ayin masu kada ƙuri'u a birni da na karkara, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
Dalilin kiran sa da 'kwamanda' ya fito ne daga salon shugabancinsa wanda ke tafiya da tsari irin na soji wajen cimma manufa, amma kuma tare da sauƙin kai da tausayi irin na farar hula.
An rahoto cewa shi mutum ne da ke bayar da umarni amma kuma yake sanya ido da kansa domin ganin an samu sakamakon da ake buƙata.

Source: Facebook
4. Tasirin naɗin Garo ga gwamnatin Abba
Ana kallon naɗin Murtala Garo a matsayin mafi dacewa a halin yanzu saboda ƙwarewarsa wajen magance matsalolin karkara da kuma sarrafa mutane.
Ta hanyar zaɓar Garo, Gwamna Abba ya buɗe wata sabuwar kofa ta haɗin kai tsakanin jam'iyyu da manyan masu faɗa-a-ji na jihar, wanda hakan zai iya ƙara haska nasararsa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamna ya gina sababbin masallatai 50 don taimakawa addinin musulunci a Najeriya
Wannan naɗi ya samu goyon bayan mambobin APC na Kano da dama, ciki har da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, ministocin Kano biyu, da kuma akasarin 'yan majalisar tarayya na jam'iyyar daga jihar.
5. Surukuntakar Murtala Garo da Atiku Kwankwaso
Murtala ya fito daga babban gida da ya yi fice a Kano wanda ya samar da 'yan siyasa irinsu Aminu Sule Garo, Nasiru Sule Garo da sauransu.
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso yana aure a gidansu, sannan The Cable ta rahoto cewa Murtala kuma suruki ne na Atiku Abubakar.
Idan aka rabu da siyasa, mai dakin Kwankwaso wato Salamatu, 'yar uwar 'dan siyasar ne, shi kuma ya yi aure a gidan Wazirin Adamawa.
Ana cewa Murtala Garo yana da kusanci sosai da mai dakin Abdullahi Ganduje da aka fi sani da goggo.
Abba ya mika sunan Garo ga Majalisar Kano
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf, ya mika sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin Kano domin tantancewa da amincewa a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.
Gwamnatin Kano ta ce nadin ya yi daidai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wanda ke bai wa gwamna ikon nada mataimakin gwamna idan aka samu gurbi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

