'A Ba Mu Sababbin Dabaru,' Sirrin Wasikar Sojojin Amurka kan Iran Ya Fito Fili

'A Ba Mu Sababbin Dabaru,' Sirrin Wasikar Sojojin Amurka kan Iran Ya Fito Fili

  • Rahotanni sun ce babban jami'in rundunar sojin Amurka ya bukaci masu nazarin leken asiri su gabatar da sababbin dabarun matsa wa Iran lamba
  • An ce an aika sakon ne ta imel domin neman "sababbin hanyoyi masu bankaye da ba a saba amfani da su ba" wajen hukunta Iran
  • Matakin ya zo ne yayin da gwamnatin Donald Trump ke fuskantar kalubale wajen cimma burinta na tilasta Iran komawa teburin tattaunawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington D.C. – Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Amurka ta fara neman sababbin dabaru daga jami'anta kan yadda za a kara matsa wa Iran lamba yayin da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ke ci gaba.

Wani babban jami'i a sashen leken asirin rundunar Amurka ta CENTCOM ya bukaci masu nazari su gabatar da sababbin shawarwari kan hanyoyin da za a hukunta Iran.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a wajen wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta rahoto cewa an aika wannan bukata ne ta hanyar imel ga dimbin jami'an leken asiri, lamarin da aka bayyana a matsayin abin da ba kasafai ake yi ba a rundunar sojin Amurka.

Me sojojin Amurka suka nema?

A cewar rahoton, jami'in ya rubuta cewa:

"Muna neman sababbin hanyoyi masu nagarta da kuma wadanda ba a saba amfani da su ba domin matsa wa Iran lamba da kuma hukunta ta."

Mai magana da yawun CENTCOM, Kyaftin Timothy Hawkins, ya tabbatar da cewa rundunar na da al'adar amfani da sababbin dabaru wajen gudanar da ayyukanta.

Rahoton Jerussalem Post ya ce Admiral Cooper kan tuntubi jami'ai ba tare da la'akari da mukamansu ba domin samun mafi kyawun dabarun gudanar da aiki.

Trump na nazarin karin hare-hare

Rahoton ya ce wannan mataki ya zo ne kafin shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar sake kai hare-hare kan Iran, kafin daga bisani ya dakatar da shirin bayan wasu shugabannin yankin Gabas ta Tsakiya sun bukaci a rage tashin hankali.

Kara karanta wannan

An fitar da jerin kasashe 50 da Trump ya laftawa wasu kudi, ciki har da Najeriya

An kuma bayyana cewa Amurka na ci gaba da nazarin yiwuwar kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran da ake zargin suna karkashin kasa.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin wani bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Sai dai rahoton ya ce masana na ganin hare-haren sama kadai ba za su isa su lalata irin wadannan cibiyoyi ba saboda yadda aka gina su a zurfin kasa, abin da zai iya tilasta amfani da sojojin kasa, matakin da ake ganin na da hadari sosai.

Amurka ta kafa sharadin biza

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da tsarin biyan kudin jingina ga masu neman wasu nau'ukan bizar kasar daga kasashe 50, ciki har da Najeriya.

Sabon tsarin ya shafi masu neman bizar kasuwanci da yawon bude ido (B1/B2), inda wasu masu neman bizar za su iya biyan kudin jingina kafin a ba su biza idan jami'in ofishin jakadanci ya bukaci hakan.

Gwamnatin Amurka ta ce za a mayar da kudin ga wadanda suka bi ka'idojin bizar kuma suka bar kasar cikin wa'adin da aka amince da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng