
Jihar Kaduna







Wani abin fashewa ya fashe a jihar Kaduna wanda ya jawo asarar rayukan mutane biyu. Lamarin ya auku ne a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce bai damu da komawa SDP da Nasir El-Rufa'i ya yi ba. Uba Sani ya ce 'yan adawa masu kokarin hadaka ba za su yi nasara ba.

NiMet ta yi hasashen ruwa da tsawa daga Lahadi zuwa Talata. Yayin da aka lissafa jihohin da abin zai shafa, hukumar ta ba mutane shawarar abin da za su yi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani mahaifi da kishiya kan daure dansu mai shekaru 7 bisa zargin daukar biskit a shagon mahaifin. An yanke kafafun yaron.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa jiga-jigan APC ba su tashi tunawa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba, sai da ya bar jam'iyya.

Hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala ya yi zargin cewa tsohon shugaban kasa, Buhari ya dauki matakin kaucewa yada labaran karya kan taronsa da su Atiku.

Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya bayyana irin goyon bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi a tafiyarsa ta siyasa.

Shugabannin APC da NNPP a mazabar Kargi a karamar hukumar Kubau sun koma jam'iyyar SDP. Ana ganin hakan na cikin tasirin Nasir El-Rufa'i a jihar Kaduna.

Yayin da 2027 ke karatowa, ‘yan siyasa na kokarin janyo Buhari cikin tafiyarsu, inda suke kai masa ziyara don neman goyon baya da tasirinsa a siyasar Arewa.
Jihar Kaduna
Samu kari