"Har Yanzu Harsashi na Jikina bayan Zanga Zangar Yunwa:" Matashin Kano

"Har Yanzu Harsashi na Jikina bayan Zanga Zangar Yunwa:" Matashin Kano

  • Wani matashi a Kano, Muhammad Alasan ya yi magana a kanhalin da ya ke ciki bayan harbin da yan sanda suka yi a lokacin zanga-zangar yunwa a 2024
  • Tun daga wancan lokaci, Muhammad ya bayyana wa Legit cewa yanzu haka akwai harsashin da aka harba a bayansa ba tare da an cire ba
  • Ya bayyana dalilan da suka sa likitoci ba su cire masa harsashin ba, tare da bayyana bukatar neman taimako daga mahukuntan da abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Muhammad Alasan, ɗaya daga cikin matasan da suka jikkata a lokacin zanga-zangar adawa da yunwa a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya ce har yanzu yana fama da matsalar harsashin da ke jikinsa.

Kara karanta wannan

Kosan Waka: An fitar da lokacin jana'izar fitaccen mawakin Gwamnan Kano

A hira da ya yi da Legit a jihar Kano, Alasan ya tabbatar da cewa har yanzu akwai harsashi a bayansa wanda aka harba masa lokacin da yake ƙoƙarin tserewa.

An harbi matashi yayin zanga-zanga a Kano a 2024
Muhammad Alasan, matashin da aka harba a jihar Kano Hoto: Muhammad Alasan
Source: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito yadda aka gudanar da zanga-zangar adawa da matsanancin halin rayuwa da jama'a suka shiga a Najeriya.

Yadda aka harbi matashin a Kano

Muhammad Alasan, mazaunin unguwar Daurawa da ke Koki a jihar Kano, ya bayyana yadda harsashin da ya ce jami'an 'yan sanda suka harba ya same shi a ranar 1 ga watan Agustan 2024, a bakin layinsu.

A cewarsa:

"A yunkurinmu na barin wajen, sai muka ji 'yan sanda suna harbi. Suka harbi Ali a goshi, ni kuma suka harbe ni a baya bayan mun juya muna tafiya ta cikin lungunanmu da ke Koki."

Ya ƙara da cewa:

"Aka kai ni asibiti. Da farko an kai ni Asibitin Nasarawa amma ba a duba mu ba, sannan aka kai mu Asibitin Aminu Kano. Shi kuwa Ali, a can Allah Ya yi masa rasuwa."

Ya ce an duba lafiyarsa tare da ba shi magunguna, amma ba a cire harsashin da ya shiga bayansa ba har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Obasanjo gori, ya tabo batun hana tsohon shugaban wa'adi na 3

Matasahi ya roki gwamnatin Kano

Muhammad Alasan ya ce tun bayan harbin da aka yi masa a ranar 1 ga watan Agustan 2024, ba a samu cire harsashin ba saboda wasu dalilai.

Muhammad Alasan ya ce akwai bukatar a kawo masu dauki
Muhammad Alasan, wanda harsashi da ke makale a bayansa Hoto: Muhammad Alasan
Source: Facebook

Matashin ya kara da cewa yanzu haka akwai wasu daga cikin hakarkarinsa biyu da ba ya aiki saboda matsalar harbin, kuma yana neman dauki.

A cewarsa:

"Sun ce ba za su yi gaggawar cire shi ba. Mu bari sai bayan wasu kwanaki idan an samu damar cirewa sai a cire. A wancan lokacin akwai abin da ya sa ba su cire ba. Bayan haka kuma akwai matsalar kuɗi."

Ya yi kira ga mahukunta da gwamnatin jihar Kano da su duba halin da yake ciki, yana mai cewa harsashin da ke jikinsa yana hana shi gudanar da harkokinsa na yau da kullum yadda ya kamata.

Kotu ta yanke hukunci kan amarya a Kano

A baya, mun wallafa cewa babbar Kotun Kano ta yanke wa Saudat Jibrin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe mijinta kwana tara kacal bayan an daura masu aure.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Kotun ta ce an tabbatar ba tare da shakka ba cewa Saudat ta ba mijinta gubar zobo kafin ta kai masa hari da wuƙa, inda lauyan gwamnati ya yaba da hukuncin, yana mai cewa ya nuna kudirin gwamnatin Kano na tabbatar da adalci.

A cewarsa, wannan hari ne ya yi sanadin mutuwar Salisu Idris, lamarin da ya sa jami'an tsaro suka fara bincike har aka kama Saudat tare da gurfanar da ita a gaban kotu, kamar yadda Legit Hausa ta taba rahotowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng