Rabi'u Kwankwaso Ya Kadu bayan Rasuwar Fitaccen Mawakin Kwankwasiyya
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa kan rasuwar fitaccen mawakin Kwankwasiyya wanda ya ba da gudummawa
- Kwankwaso ya ce gudunmawar Kosan Waka wajen da yada manufofin tafiyarsu ba za ta taba gushewa ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da tunawa da shi
- Tsohon gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi Aljannatul Firdaus, tare da mika ta'aziyya ga iyalansa da abokansa masu alhini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga jimami a jihar Kano bayan sanar da rasuwar wani fitaccen mawakin Kwankwasiyya bayan fama da rashin lafiya.
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana alhininsa bayan samun labarin rasuwar fitaccen mawaki, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka a cikin wani takaitaccen rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi 2 ga watan Agustan 2026.
Kwankwaso ya yi ta'aziyyar rasuwar Kosan waka
Kwankwaso ya bayyana rasuwar mawakin a matsayin babban rashi, yana mai cewa mutuwarsa ta girgiza shi da sauran wadanda suka san irin gudunmawar da ya bayar.
A cikin sanarwar, Kwankwaso ya ce Kosan Waka ya taka muhimmiyar rawa wajen yada manufofi da akidun tafiyarsu ta siyasa.
Ya ce irin kokari da jajircewar marigayin wajen tallafa wa tafiyar ba za su taba mantawa da su ba, domin ya bayar da gagarumar gudunmawa.
Kwankwaso ya kuma yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Ya bayyana cewa yana fatan Allah Ya ba iyalan marigayin, abokansa da dukkan masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.

Source: Facebook
Babban rashin da aka yi na fitaccen mawakin
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce mutuwar Kosan Waka ta bar gibi a zukatan wadanda suka yi aiki tare da shi da kuma masu sha'awar wakokinsa.
A karshe, Kwankwaso ya sake mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da abokansa, yana addu'ar Allah Ya ba su karfin gwiwar jure wannan lokaci na bakin ciki.
Sanarwar ta ce:
"Na yi matuƙar alhini da jin labarin rasuwar fitaccen mawaƙi Muhammadu Buhari (Kosan Waka) a yau.
"Gudunmawar da Kosan Waka ya bayar wajen bunƙasa manufofin tafiyarmu ba za a taɓa mantawa da ita ba. Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
"Ina miƙa ta'aziyyata ta zuciya ga iyalansa da abokansa a wannan lokaci mai cike da jimami."
Abba ya yi ta'aziyyar rasuwar Kosan Waka
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana girman rashin da aka yi bayan an sanar da rasuwar fitaccen mawakin siyasa, Muhammadu Buhari.
An sanar da rasuwar mawakin da aka fi sani da Kosan Waka a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli, 2026 yana da shekara 47 bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Gwamnan ya mika ta'aziyyarsa, yayin da aka sa lokacin jana'izar marigayin da za a yi a yau a ƙauyen Tsanni, ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng
