Nasir El Rufai Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

Nasir El Rufai Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

  • Wani jigo a jam'iyyar ADC kuma na kusa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana game siyasar tsohon ministan a 2027
  • Hayatudeen Lawal Makarfi ya bayyana cewa El-Rufai yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ya ce shirye-shirye sun kankama
  • Sai dai kuma, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun El-Rufai, ya karyata wannan ikirari na Hayatudeen, tare da fayyace gaskiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Wani da aka rahoto cewa na kusa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya yi karin haske game da siyasar tsohon ministan a Najeriya.

Hayatudeen Lawal Makarfi ya bayyana cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 mai zuwa.

An fara maganar takarar Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna a taron jam'iyyar ADC, Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Na kusa da El-Rufai ya magantu kan siyasar Malam

Hayatudeen Lawal Makarfi, wanda aka sani a matsayin mutumin El-Rufai, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a wani bidiyo da The Nation ta gano.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamnan jihar Kano, Shekarau ya fice daga jam'iyyar PDP

Ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai mika mulki ne ga tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a watan Mayun shekarar 2027 da ake tunkara.

Jigon jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ya ce shirye-shiryen sun riga sun kankama domin ci gaba da neman amincewar al'umma game da zaben 2027.

A cewarsa:

“Mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai mika mulki ga Malam Nsir El-Rufai a shekarar 2027 a watan Mayu. An riga an fara tafiya zuwa kan kujerar shugaban ƙasa."

An karyata zancen takarar El-Rufai

Amma a hannu daya, mai magana da El-Rufai, Mr Muyiwa Adekeye, ya karyata wannan magana ta Hayatudeen, yana mai cewa, ba da yawun tsohon gwamnan aka yi ta ba.

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Adekeye ya ce:

"Mallam Nasir El-Rufai ya nesanta kansa daga duk wasu maganganu da ake yi da suka shafi burinsa na siyasa, musamman maganar wani da ake cewa abokin siyasar Malam ne. Lallai ba shi ne ya bada umarnin yin wadannan maganganu ba."
Na kusa da El-Rufai ya magantu kan takarar malam a 2027
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Yadda ake zargin cin zarafin El-Rufai

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi da jam'iyyar da za ta iya kayar da APC a zaben 2027

Hayatudeen dai ya nuna cewa akwai tsari mai karfi da ake ginawa tun yanzu a sansanin siyasar Nasir El-Rufai wanda ake zargin APC na ci gaba da yi masa bita da kullin siyasa.

El-Rufai na daga cikin wadanda suka tallata APC da dan takararta a zaben shekarar 2023, Bola Ahmed Tinubu ido a rufe domin tabbatar da mulki ya koma Kudu saboda a cewarsa hakan shi ne adalci.

Daga baya, El-Rufai ya yi nadamar tallata Tinubu a zaben 2023 inda ya ce ya yi abin da ya yi ne don Allah, ƙasa da jam’iyya ne ba tare da tsammanin samun komai daga kowa ba.

El-Rufai ne dai dai da Najeriya

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu 'yan Najeriya game ra'ayinsu kan wannan jita jita ta takarar El-Rufai.

Abba Hassan Gezawa:

"Wallahi El-Rufai ne dai dai da Najeriya. Ai bahaushe ya ce karan bana shi ke maganin zomon bana. Kowa ya shaida shi mutum ne mai fada a cika, kuma mai bin ka'idoji wajen yin aiki, don haka, zai shimfida ayyuka a Najeriya, amma fa zai rusa wadanda ke gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba."

Kara karanta wannan

Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa

Amina Lawal Mailafiya:

"Ni 'yar Kaduna ce, kuma yayata na daya daga cikin malaman da El-Rufai ya kora daga aiki, amma duk da haka, dole ne mu yi masa adalci, in dai a bangaren gina kasa ne, to babu kamarsa. Ka ga, idan ya zama shugaban kasa, kowa zai ji a jikinsa, amma kuma za a ga ayyuka a kasa. A mulkinsa ne za a yi asalin masu gudu su gudu."

Kalli bidiyon bayanin Hayatudeen a kasa:

Tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya samu beli

A wani labarin, an ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya halarci zaman kotu a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026.

A yayin zaman kotun, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya samu beli wanda zai sanya ya bar hannun hukumomin tsaron da ke ci gaba da tsare shi.

Dan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, wanda yake dan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun cika sharuddan belin da aka ba mahaifinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com