Ana So Atiku, Peter Obi, Kwankwaso da Manyan Yan Adawa Su Goyi Bayan Mutum 1 a Zaben 2027
- Kungiyar G100 ta bukaci shugabannin adawa su hada kai su tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya a zaben 2027
- Kungiyar ta kaddamar da shirin Doctrine of a Necessary Democratic Opposition domin karfafa adawa a Najeriya
- Ta ce za ta kira taron shugabannin adawa cikin makonni biyu masu zuea domin cimma matsaya daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wata hadakar fitattun 'yan Najeriya 100 daga bangaren jam'iyyun adawa, sun ja hankalin Atiku Abubakar, Peter Obi, Gwamna Seyi Makinde, Rabiu Kwankwaso kan zaben 2027.
Hadakar, wacce ta kunshi kungiyoyin fararen hula, masana da masu tsara manufofi ta bukaci jagororin adawa su hada kai tare da tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya domin fuskantar zaben 2027.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce domin cimma wannan buri, kungiyar ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna Doctrine of a Necessary Democratic Opposition, wanda aka ce zai taimaka wajen karfafa bangaren adawa
Fitattun mutane sun amince da shirin
Daga cikin wadanda suka sanya hannu kan wannan matsaya akwai Salihu Lukman, Hon. Nnena Ukeje, Elder Simon Achuba, Dr. Akilu Indabawa, Hon. Annie Ekeh, da Prof. Anthony Kila.
Sauran sun kunshi Dr. Awalu Anwar, Dr. Emeka Ejikonye, Dr. Ibrahim Moddibo, Dr. Ladan Salihu, Dr. Ayokunle Fagbemi, Salihu Tanko Yakasai, Zainab Buba Galadima da Hon. Sergios Ogun, da sauransu.
Kungiyar ta ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta ba na tattalin arziki ko siyasa kadai ba ne, illa matsaloli ne da suka shafi tsarin kasa baki daya.
Ta bayyana cewa ba za a samu cikakken gyara ba sai an samu bangaren adawa mai karfi, hadin kai da kuma kishin kasa wanda zai rika dorawa gwamnati alhakin ayyukanta.
G100 ta shawarci manyan yan adawa
Kungiyar ta bukaci manyan shugabannin adawa a Najeriya da su jingine duk wani banbanci da burikansu na kashin kai, su hada kai wuri guda.
Daga cikin sunayen jiga-jigan da kungiyar ta ambata akwai Sanata David Mark, Atiku Abubakar, Peter Obi, Gwamna Seyi Makinde, Gwamna Bala Mohammed, Sanata Seriake Dickson, Rotimi Amaechi, da Sanata Rabiu Kwankwaso.
"Rabuwar kai ba za ta kawo nasara ba"
Kungiyar ta yi tambaya kan yadda bangaren adawa ke sa ran kayar da jam'iyya mai mulki alhali ba ta iya hada kanta ba, kamar yadd Leadership ta kawo.
Ta ce:
"Lokaci ya yi da za a daina fifita muradun kai. Najeriya ba za ta samu ceto daga shugabannin adawa da ke tafiya kowa da gabansa zuwa ga rashin nasara ba."
A matsayin wani bangare na sabon shirin, G100 ta sanar da cewa cikin makonni biyu masu zuwa za ta kira taron National Council of Opposition Leaders, wanda zai hada shugabannin adawa daga sassan Najeriya.

Source: Twitter
A taron, ana sa ran za a tattauna kan tsarin hadin kai, dabarun siyasa da kuma yadda za a samar da dan takarar shugaban kasa guda daya.
Salihu Lukman ya gargadi yan adawa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon jigo a jam'iyyar ADC, Salihu Lukman ya yi gargadin cewa yana adaw na shirin tafka kuskure a zaben 2027.
Lukman ya bayyana damuwa cewa rashin hadin kai tsakanin shugabannin adawa zai iya tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Ya bayyana cewa Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi suna daga cikin shugabannin da ya kamata su ajiye burinsu domin samar da hadin kai.
Asali: Legit.ng


