Sojoji Sun Gano Inda aka Boye Gawar Shugaban Al'umma da aka Hallaka a Imo
- Dakarun sojojin Najeriya sun tono gawar marigayi Cif Ibe Anyadu daga wani kabari marar zurfi a dajin Umudike na jihar Imo
- Ana zargin wasu da aka kama kan laifuffukan ta'addanci ne suka kashe shugaban al'ummar, kuma ɗaya daga cikinsu ne ta tona asiri
- Gano gawar ya kawo kwanciyar hankali game da batun da ya dade yana daga hankalin yan uwa da iyalan marigayin yayin da ke bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Imo – Dakarun Operation UDO KA na rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumar nasara bayan sun gano tare da tono gawar marigayi Cif Ibe Anyadu na al'ummar Aggah a jihar Imo.
A cewar rundunar, ana zargin marigayin ya mutu ne bayan wasu 'yan ta'adda da aka kama kwanan nan bisa laifuffuka a yankin sun kashe shi.

Source: Original
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da rundunar ta fitar, tare da wallafa a shafinta X ya ce ci gaban ya biyo bayan wasu hare-haren da jami'an tsaro suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
An kama masu laifi a Imo
Samarwar ya kara da cewa binciken ya kai ga cafke waɗanda ake zargi da kashe wani sojan Najeriya tare da ƙwace makaman aikin soja da aka sace.
Rundunar ta ce yayin bincike, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya amsa hannu a kisan Cif Anyadu, sannan ya amince ya kai dakaru zuwa wurin da aka binne gawar.
A ranar 2 ga Agustan 2026, waɗanda ake zargin suka jagoranci sojojin zuwa wani kabari marar zurfi da ke cikin dajin Umudike, wanda ake zargin yana ɗaya daga sansanonin masu laifin. A nan ne aka tono gawar marigayin.
An gudanar da aikin tono gawar ne a gaban 'yan uwan mamacin, jami'an kungiyar sintiri ta Ohaji/Egbema, da wakilan al'ummomin Aggah da Umudike.
Imo: Ana binciken masu laifi
Iyalan mamacin sun kawo akwatin gawa da motar ɗaukar gawa domin a yi masa jana'iza cikin mutunci bisa al'adunsu na jihar Imo kuma a matsayinsa na shugaba a jihar Imo.
Kwamandan Joint Task Force South-East Operation UDO KA, Manjo Janar Oluremi Ayobami Fadairo, ya jajanta wa iyalan mamacin tare da yi masa addu'ar samun rahama.

Source: Facebook
Ya kuma tabbatar musu da cewa za a yi adalci, inda ya ce:
"Za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu domin su fuskanci hukunci daidai da dokokin Tarayyar Najeriya."
Rundunar Operation UDO KA ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Kudu maso Gabashin Najeriya ta hanyar tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Jirgi ya yi hadari a Imo
A baya, kun samu labarin cewa wani karamin jirgin sama kirar Cessna 172 ya gamu da hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu matsala a sararin samaniya tare da jefa jama'a a cikin fargaba.
Jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Port Harcourt ya yi kokarin sauka a Owerri babban birnin jihar Imo saboda matsalar da ya samu, amma ya yi hatsari inda jama'a suka shiga wani hali.
Saboda wannan matsalar, suka karkatar da jirgin zuwa Owerri domin yin saukar gaggawa, amma sai ya rikito kafin saukar tasa ta kammala, kuma hukumar NSIB ta ce gobara ba ta tashi ba bayan hatsarin.
Asali: Legit.ng


