APC Ta Rikita Lissafin 'Yan Adawa a Kano, Gwamna Abba Ya Aika Sako ga Malam Shekarau
- Gwamna Abba Kabir ya bayyana farin cikinsa da sauya shekar Malam Ibrahim Shekarau, yana mai cewa hakan ya karawa APC karfi a Kano
- Abba Gida-Gida ya ce nan ba da jimawa ba za a shirya taron karbar tsohon gwamnan zuwa APC bayan an gama shirye-shirye a matakin kasa
- Gwamnan ya jaddada cewa APC ta shirya tsaf domin lashe dukkan kujerun zaɓe a zaɓukan da ke tafe a shekarar 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi maraba da tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau, zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP, kuma majiyoyi sun tabbatar da cewa ya koma APC da ya bari a 2018.

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027

Source: Facebook
Gwamna Abba ya yi maraba da Shekarau a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi, cewar Channels tv.
Abba Gida-Gida ya bayyana dawowar Shekarau a matsayin babban ƙari ga ƙarfin jam’iyyar APC a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
Jam'yyar APC na ƙara ƙarfi a jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce nan ba da jimawa ba za a sanya ranar karɓar tsohon gwamnan a hukumance cikin APC, bayan tuntubar sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC a Kano na ci gaba da samun ƙarin goyon baya da haɗin kai, lamarin da ke ƙara tabbatar da ita a matsayin mafi rinjaye a siyasar jihar Kano.
Gwamnan ya jaddada cewa APC ta shirya tsaf domin lashe dukkan kujerun zaɓe a zaɓukan da ke tafe, yana mai danganta hakan da haɗin kai da dabarun siyasa da jam’iyyar ke bi.
Gwamna Abba ya aika sako ga 'yan APC
Ya kuma tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya baya cewa gwamnati da shugabanni jam'iyya na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai a cikin gida tare da faɗaɗa tasirin jam’iyyar a matakin ƙasa da ƙasa.
Gwamna Abba Kabir ya buƙaci mabiya jam’iyyar APC su ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da ƙara wayar da kai domin shirye-shiryen tunkarar zaɓuka masu zuwa a shekarar 2027.
A ranar Lahadi ne Shekarau ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a gidansa da ke Kano, tare da bayyana komawarsa APC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Source: Facebook
Shekarau ya rike kujerar gwamnan Kano daga 2003 zuwa 2011, sannan ya riƙe muƙamin ministan ilimi tsakanin 2014 zuwa 2015.
Daga 2019 zuwa 2023, ya kasance sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.
Gwamna Abba ya yi maraba da wannan mataki da Shekarau ya dauka, yana mai cewa dawowarsa ta karawa APC karfi a Kano.
APC ta Kano na tare da Shugaba Tinubu?
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta fito ta musanta batun janye goyon bayanta ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
APC ta ƙaryata wata sanarwa da wata ƙungiya mai suna Arewa APC Forum reshen jihar Kano ta fitar, tana iƙirarin janye goyon baya ga Shugaba Tinubu.
Jam’iyyar mai mulkin Kano ta jaddada cewa babu wani sashe na jam’iyyar APC da tsarin mulki ya ba damar ɗaukar wannan mataki, inda ta jaddada goyon baya ga shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

