Dalilan da Suka Sanya Abba zabar Garo a Mataimakin Gwamnan Kano

Dalilan da Suka Sanya Abba zabar Garo a Mataimakin Gwamnan Kano

  • Ana cigaba da tattaunawa kan yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zabi Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan Kano
  • Murtala Garo na daya daga cikin mutanen da masu ruwa da tsaki na APC suka tura wa Abba Kabir, kuma yana cikin na kusa da Abdullahi Ganduje
  • A yanzu haka dai kallo ya koma kan Majalisar Kano kan yadda za su tantance Garo duk da wasu zarge-zarge da gwamnatin Abba Kabir take yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tura sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar Kano domin tantancewa da amincewa a matsayin mataimakin gwamna.

Gwamnan ya ce matakin ya yi daidai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Abdussalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Alƙawarin da Garo ya yi wa Abba da 'yan Kano bayan zabo shi ya zama mataimakin gwamna

Abba Kabir Yusuf da Murtala Sule Garo
Abba Kabir Yusuf a hagu, Murtala Sule Garo a dama. Hoto: Murtala Sule Garo|Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Dalilin zabar Murtala Garo da gwamna ya yi

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana ganin nadin Murtala Garo ya samo asali ne daga cikin tsare-tsaren siyasa a Kano da ma kasa baki daya.

An san Garo a matsayin na kusa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda a karkashinsa ya taba zama kwamishina.

Tasirinsa a wancan lokaci ya sa ake yi masa lakabi da “Kwamanda” a harkokin siyasar jihar Kano, wanda ake ganin zai taka rawa sosai a tazarcen Abba Kabir a 2027.

Ana kuma ganin yana da karbuwa a tsakanin al’umma, musamman a yankin Kano ta Arewa, kuma yana da alaka da ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban, lamarin da masana ke cewa ya iya zama daya daga cikin dalilan daukarsa.

Majiyoyi daga fagen siyasa sun ce nadin nasa ya biyo bayan shawarar manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da wasu kungiyoyi a jam’iyyar APC, wadanda suka zabe shi cikin jerin wasu mutane kafin gwamnan ya yanke hukunci na karshe.

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Murtala Sule Garo da Abba Kabir Yusuf
Murtala Garo na gaisawa da gwamnan Kano a wajen taro. Hoto: Murtala Sule Garo
Source: Facebook

Garo ya fitar da wani sako a shafinsa na Facebook yana mika godiya ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan amincewa da shi da ya yi a matsayin mataimaki.

Zarge-zargen da aka yi wa Garo

Nadin Garo ya sake tayar da muhawara kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka shafi aikin gwamnati da ya yi a baya.

A baya EFCC ta bincike shi kan zargin badakalar kudi a lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta a gwamnatin Ganduje.

Duk da lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, babu rahoton da ya tabbatar da hukuncin kotu a kansa, yayin da magoya bayansa ke cewa zarge-zargen na da alaka da siyasa.

Takarar Yusuf Buhari ta kankama

A wani labarin, mun kawo muku cewa dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari ya kara kaimi wajen neman takara a zaben 2027.

Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Kastina sun takawa Yusuf Buhari baya wajen zuwa gidan gwamnati da ganawa da gwamna Dikko Radda.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya bayyana cewa jama'a ne suka sanya Yusuf Buhari ya tsaya takara ba wai shi ya saka kan shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng