Abun Bakin ciki: Yadda 'Yan Fashi Suka Kashe Dalibar Ajin Karshe a Jami'ar Lafia

Abun Bakin ciki: Yadda 'Yan Fashi Suka Kashe Dalibar Ajin Karshe a Jami'ar Lafia

  • Iyali, abokai da al'ummar Jami'ar FULAFIA sun yi jana'izar Habiba Ummi Lele da aka harbe har lahira yayin dawowa daga bikin yaye ɗalibai
  • Mutuwar ɗalibar ta ƙara tayar da hankula kan matsalar tsaro a Nasarawa, bayan sace wasu ɗalibai uku na jami'ar kwanaki kaɗan da suka gabata
  • 'Yan Najeriya sun cika kafafen sada zumunta da saƙonnin ta'aziyya da kira ga gwamnati ta ɗauki matakan inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Nasarawa - An yi jana'izar ɗalibar aji na 400 a sashen ilmin sinadarai na Jami'ar Tarayya da ke Lafia (FULAFIA), Habiba Ummi Lele, wadda ake zargin 'yan fashi da makami sun kashe a jihar Nasarawa.

Habiba ta rasa ranta ne a ranar Asabar bayan wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne suka buɗe wa motar da take ciki wuta yayin da take dawowa Lafia daga bikin yaye wata kawarta a Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha da ke Keffi.

Kara karanta wannan

Farfesa Safiyanu Ishiaku ya kare Musulunci daga jingina masa ta'addanci

'Yan fashi sun kashe wata dalibar ajin karshe a jami'ar Lafia
Habiba Ummi Lele, dalibar ajin karshe a jami'ar Lafia da 'yan fashi suka kashe. Hoto: Elizabetholu
Source: Facebook

Jana'izar dalibar da aka kashe

An gudanar da jana'izar Habiba a ranar Lahadi a gidan ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar mazabar Awe ta Arewa, Hon. Hudu A. Hudu Kanje, da ke garin Kanje, in ji rahoton Daily Trust.

Shugaban ƙaramar hukumar Awe, Hon. Umar Abubakar Dan'Akano, da Hon. Hudu Kanje na daga cikin manyan jami'an da suka halarci sallar jana'izar.

Iyalan marigayiyar, abokanta, shugabannin al'umma da sauran masu alhini sun taru domin yi mata addu'a tare da jajanta wa iyalanta bisa wannan babban rashi.

Mutuwar dalibar ta girgiza 'yan Najeriya

Mutuwar Habiba ta jawo jimami a kafafen sada zumunta, inda 'yan Najeriya da dama suka bayyana alhininsu tare da nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara.

Wani mai amfani da Facebook, Mujahid Saleh Saad, ya yi addu'ar Allah Ya gafarta mata, Ya ba iyalanta, abokanta da al'ummar FULAFIA haƙurin jure wannan rashi.

Kara karanta wannan

'Fulani ba 'yan ta'adda ba ne,' Sarkin Musulmi ya yi magana kan matsalar tsaro

A nata ɓangaren, Stephiny Ugomma ta bayyana takaicinta, tana mai cewa samun labari mai daɗi a Najeriya a yanzu ya zama abin godiya.

Shi ma Tony Ocheni ya yi Allah wadai da matsalar tsaro, yana mai cewa yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya ya zarce na wasu ƙasashen da ke fama da yaƙi.

An sake kira a ƙara tsaro

Mutuwar Habiba ta zo ne kwanaki kaɗan bayan da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace ɗalibai uku na matakin 100 na FULAFIA daga wani masaukin ɗalibai da ke Bukan Kwato a Lafia.

An yi jana'izar dalibar jami'ar Lafia da 'yan fashi suka kashe
Taswirar jihar Nasarawa, inda 'yan fashi suka kashe dalibar ajin karshe a jami'ar Lafia. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da daddare, inda suka tafi da ɗaliban, lamarin da ya ƙara tayar da fargaba kan tsaron ɗaliban da ke zaune a wajen harabar jami'a.

Waɗannan hare-hare guda biyu sun sa ɗalibai, iyaye da mazauna jihar suka sake yin kira ga jami'an tsaro da gwamnatin jihar Nasarawa da su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan harin da ya yi sanadin mutuwar Habiba ba, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto ɗaliban da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com