Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani kan Mata da Jarirai a Wani Kazamin Hari a Katsina
- 'Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da raunata akalla mutum bakwai a kauyen Shuwaki da ke Bakori a jihar Katsina
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi garkuwa da mutane 32, amma daga bisani suka saki mace guda saboda rashin lafiya
- Tsohon shugaban karamar hukumar Bakori ya ce mafi yawan wadanda aka sace mata ne, wasu kuma dauke da jarirai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - 'Yan bindiga sun kashe wani mazaunin kauyen Shuwaki da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina tare da raunata akalla mutum bakwai.
Maharan sun kuma yi garkuwa da mutane 32, sai dai daga bisani suka saki mace guda saboda rashin lafiya, lamarin da ya rage adadin wadanda ke hannunsu zuwa 31.

Source: Original
Tsohon shugaban Bakori ya yi karin bayani
Tsohon shugaban karamar hukumar Bakori, Aminu Magaji, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata hira da aka yi da shi, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Ya ce 'yan bindigar sun shiga kauyen Shuwaki da ke mazabar Jargaba tsakanin karfe 9:00 zuwa 9:45 na daren ranar Asabar, inda suka kwashe tsakanin awa daya da rabi zuwa biyu suna cin karesu
A cewarsa:
"Sun kashe mutum daya sannan suka jikkata akalla mutum bakwai, sun kuma kwashe shanu da tumaki tare da yin garkuwa da mutane 32."
Yan bindiga sun sako mace 1
Magaji ya ce bayan sun yi nisa da kauyen, maharan sun saki daya daga cikin matan da suka sace saboda rashin lafiyarta da ya hana ta ci gaba da tafiya.
Ya ce bayanan da aka samu daga kauyen Doma sun nuna cewa 'yan bindigar sun nufi cikin daji da sauran mutanen da suka sace.
Ya bayyana cewa mafi yawan wadanda ke hannun maharan mata ne, wasu daga cikinsu kuma suna dauke da jarirai.
Har zuwa lokacin da ya yi wannan bayani, babu wata sanarwa ko bukatar kudin fansa da aka samu daga wajen maharan.
Kokarin jami'an tsaro bai yi nasara ba
Tsohon shugaban karamar hukumar ya ce maharan sun kwashe wayoyin hannu daga hannun mazauna kauyen da kuma wuraren cajin waya.
Ya ce wasu da suka kira wayoyin da aka sace sun samu wadanda suka amsa suna cewa wayoyin suna hannun 'yan bindigar.
A cewarsa, jami'an tsaro sun isa yankin da motoci akalla biyar, amma ba su samu damar cafke maharan ko ceto mutanen da aka sace ba.
A rahoton Aminiya, Magaji ya ce:
"Jami'an tsaro sun yi duk mai yiwuwa, amma ba su samu damar hana su tafiya da mutanen ba."

Source: Facebook
Hare-hare sun fara korar mutane
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce harin Shuwaki ya biyo bayan hare-haren da aka kai kauyukan Unguwar Dogo da Alhazawa a daren Juma'a.
Ya shaidawa Legit Hausa cewa mutum daya ya samu munanan raunuka a hare-haren, yayin da aka sace dabbobi da wasu kadarori.
A cewarsa, tun daga karshen watan Yuli, an kai hare-hare da dama a kauyukan Bakori, lamarin da ya yi sanadin kashe mutane, sace wasu da kuma kwashe dabbobi.
"Kowa a Shuwaki yana cikin tsoro. Wasu sun fara kwashe kayansu suna barin yankin," in ji shi.
Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 60
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tare da hadin gwiwar 'yan sa kai da mafarauta na musamman sun kashe sama da 'yan bindiga 60.
Jami'an sun kuma yi nasarar kwato makamai da sauran kayayyaki da 'yan bindigar suka bari, amma duk da nasarar an samu asarar rayukan zaratan ma'aikata
Asali: Legit.ng


