Abubuwan da Ya Kamata a Sani game da Yarjejeniyar da Aka Yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
A ranar 11 da 12 ga watan Agusta, 2026, Kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'a Wa'Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya kuma ta gudanar da wani babban taro na kasa da kasa kan zaman lafiya a Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kungiyar JIBWIS wacce aka fi sani da Izala a Najeriya ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar Kungiyar Kasashen Musulmi ta duniya karkashin jagorancin Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa.

Source: Facebook
Izala ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook mai dauke da bayanin abubuwan da aka gudanar a taron.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin addinan Musulunci da Kiristanci, malamai da masana, masu yanke shawara da kuma wakilan hukumomin gwamnati.
Haka zalika ƙungiyoyin farar hula, hukumomin yanki da na ƙasa da ƙasa da kuma wasu fitattun mutane daga Najeriya, Afirka ta Yamma da sauran ƙasashen duniya sun halarci taron.
An yi wa taron take da, "Bambancin Addini da Al’adu da Zaman Lafiyar Al’umma: Haɗin Gwiwa Domin Kyakkyawar Makoma," kuma ya gudana ne karkashin kulawar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka ka hankali a taron shi ne yarjejeniyar fahimtar juna da Musulmi da Kiritocin Najeriya suka rattaba hannu a kai.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da wannan yarjejeniya ta zaman lafiya da aka kulla a taron da Izala ta gudanar.
Rattaba hannu kan yaarjejeniyar Musulmai da Kiristoci
Shugabannin addinin Musulunci da Kiristoci fiye da 50 ne suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar ta zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a Najeriya.
Daga ciki akwai shugaban JIBWIS na Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugabannin ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI), shugabannin Kiristoci da wakilan gwamnatin Najeriya.
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III na cikin wadanda suka rattaba hannu.
An gina wannan yarjejeniya ne domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Kiristoci da Musulmi, wanda ana ganin hakan muhimmin abu ne musamman saboda halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya aika saƙo na musamman ga Musulmai da Kiristocin Najeriya
Shugabannin addinai sun karbi matakin
A jawabinsa, Sakatare Janar na ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, ya bayyana cewa dukkanin mabiya addinan biyu na maraba da wannan yarjejeniya.
"Kowane bangare ya san cewa tsattsauran ra'ayi ya cutar da kowa; kowa ya ga matsalar hakan," in ji shi.
A rahoton da BBC Hausa ta wallafa, shugaban ƙungiyar shugabannin Kisirocin Arewa, John Praise Daniel ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta rage furta kalaman rarrabuwar kawuna daga wasu malamai.

Source: Facebook
Sharudan da aka gina yarjejeniyar a kansu
Bayan rattaba hannu a kan yarjejeniyar, kungiyar JNI ta bayyana cewa akwai wasu abubuwa hudu da aka kafa wannan yarjejeniya a kansu domin cimma manufar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci a Najeriya.
1. Kafa kungiyar hadaka
Shugabannin addinan biyu sun amince za a kafa wata kungiyar hadin gwiwar Musulmi da Kiristoci, wanda za ta yi aiki ba tare da nuna bambanci ba wajen hada kan al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan
Duk da yi masu gorin tikitin Muslim Muslim, Kiristoci sun shirya abin alheri ga Tinubu
Sun ce hakan zai yiwu ne idan shugabannin addinai, hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin farar hula suka haɗa ƙarfi cikin kishin ƙasa, mutunta juna da bin ƙa’idojin addini da ɗabi’a da aka yi tarayya a kansu.
2. Gyara da bunkasa fannin ilimi
Haka zalika jagororin addinann biyu sun yarda da bullo da wani tsari da zai gyara tare da bunkasa bangaren koyo da koyarwa musamman yadda malamai ke gudanar da wa'azi.
Yarjejeniyar ta tanadi inganta yadda malamai ke koyarwa da da'awa a minbari domin kaucewa furta maganganun da zasu iya hadda rabuwar kawuna tsakanin yan Najeriya.
3. Dakatar da furta kalaman kiyayya
Wani abu da ya dade yana jawo fabuwar kai tsakanin manyan addinan Najeriya shi me yadda wasu mabiya addini da malamai ke amfani da kalaman da ke cusa kiyayya tsakanin yan Najeriya.
Bisa haka ne sabuwar yarjejeniyar ta umarci bangarorin biyu da su tsawataraa malamai su kiyaye amfani da irin wadannan kalamai da ke tunzura mabiyansu da ku sanya kiyaye tsakanin Musulmai da Kiristoci.
4. Bunkasa rayuwar matasa
A wurin taron da aka gudanar, an amince da shirin Sakatare-Janar na Ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Sheikh Dr Mohammed Al-Issa, mai taken “Nigerian Youth for Peace” wato matasa Najeriya don zaman Lafiya.
Shirin zai yi aiki tare da kwamitin haɗin gwiwar da aka tsara, inda zai gudanar da ayyukansa a dukkan shiyyoyin shida na Najeriya tare da yaɗa sakamakon ayyukansa ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Bayan wannan, yarjejeniyar ta kunshi bullo da wasu tsare-tsare da wasu wayar da kan matasa kuma su taimaki rayuwarsu ta hanyar samun ilimi domin kauce aa fadasa tarkon masu kokarin cuta kiyayya a tsakaninsu.

Source: Facebook
Yadda za a aiwatar da yarjejeniyar
Da yake jawabi bayan taron, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce Izala da kungiyar Kasashen Musulmi tta duniya za su kafa kwamitin da zai gabbatar da an cika alkawurran da aka dauka.
Ya kuma ce ba za a bar sanarwar da aka fitar bayan taron a matsayin rubutu kawai ba, inda ya bayyana cewa za a kafa kwamitin aiwatarwa da zai sa ido kan yadda ake gudanar da abin da aka amince da shi, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
An ja hankalin Musulmi da Kiristoci
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci Musulmi da Kiristoci su mutunta addinan juna.
Bala Lau ya bukaci ‘yan Najeriya su koyi darasi daga rayuwar Annabi Muhammad, wanda ya ce ya zauna lafiya da mabiyan sauran addinai a Madina.
Ya ce Musulmi da Kiristoci duk suna da hakki a Najeriya kuma ya kamata su zauna lafiya duk da bambancin addininsu, yana ami cewa babu wani addini da zai iya korar wani daga Najeriya.
Asali: Legit.ng


