Sheikh Abdullahi Bala Lau Ya Aika Sako na Musamman ga Musulmai da Kiristocin Najeriya
- Shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci Musulmi da Kiristoci su mutunta addinan juna
- Babban malamin musuluncin ya ce babu wani addini da ke da ikon korar mabiyin wani addini daga Najeriya
- Ya bayyana cewa kungiyar JIBWIS da Majalisar musulmin duniya za su kafa kwamiti domin aiwatar da kudurorin taron zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci ‘yan Najeriya su mutunta addinan juna tare da hada kai wajen kare kasar.
Ya ce Musulmi da Kiristoci duk suna da hakki a Najeriya kuma ya kamata su zauna lafiya duk da bambancin addininsu.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda ta kaya tsakanin wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC

Source: Facebook
Daily Trust ta ce, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a filin jirgin saman Abuja, bayan tashin Sakataren Janar na Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League), Sheikh Dr Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa.
Sakon Bala Lau ga Musulmi da Kiristoci
A cewar Bala Lau, an shirya taron hadin gwiwa kan zaman lafiya ne domin inganta zaman lafiya, fahimtar juna da kwanciyar hankali a Najeriya, Yammacin Afirka da sauran sassan nahiyar Afirka.
Ya ce bambancin al’umma bai kamata ya hana ‘yan Najeriya cimma burin zaman tare cikin lumana ba.
“Duk da bambancin da ke tsakaninmu, muna da buri guda, muna da buri guda na tabbatar da cewa muna rayuwa cikin zaman lafiya da jituwa. Kai ka yi addininka, ni kuma na yi nawa. Babu tilastawa a cikin addini,” in ji shi.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya na cikin alheri, an turo musu tallafin fiye da Naira biliyan 40 daga ƙasar waje
Malamin Ya ce Najeriya ta kowa ce
Bala Lau ya ce babu Musulmi ko Kirista da ke da ikon korar wani daga Najeriya, yana mai jaddada cewa kasar ta kowa ce.
“Me za mu yi? Dole ne mu mutunta addininmu. Kai ka mutunta addinina, ni kuma na mutunta naka. Kuma mu kare kasarmu. Kasar tamu ce,” in ji shi.
Bala Lau ya bukaci ‘yan Najeriya su koyi darasi daga rayuwar Annabi Muhammad, wanda ya ce ya zauna lafiya da mabiyan sauran addinai a Madina.
Izala za ta kafa kwamitin hadin kai
Ya kuma ce ba za a bar sanarwar da aka fitar bayan taron a matsayin rubutu kawai ba, inda ya bayyana cewa za a kafa kwamitin aiwatarwa da zai sa ido kan yadda ake gudanar da abin da aka amince da shi.

Source: Facebook
Ya ce kungiyar JIBWIS da Muslim World League za su kafa wani dandali na hadin gwiwa domin bibiyar alkawuran da ke cikin sanarwar taron.
“Mu shugabannin addini ne da shugabannin ruhaniya. Dole ne mu bi abin da muka fada. Dole ne mu aiwatar da abin da muka fada domin mutane su yi koyi da mu,” in ji shi.
Sheikh Jingir ya kare matsayarsa
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske kan goyon bayansa ga tikitin muslim-muslim.
Sheikh Jingir ya bayyana cewa ya daɗe yana goyon bayan a samu shugaban ƙasa musulmi kuma mataimakinsa musulmi, tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Malamin addinin ya bayyana cewa yana da 'yancin ya zabi abin da yake so, kuma yana da 'yancin ya tallata musulunci.
Asali: Legit.ng
