Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Tara Malaman Izala, Darika da Sarakuna a Kaduna
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar ya jagoranci taron Gidauniyar Sultan a Kaduna a ranar Talata
- Manyan sarakunan Arewa kamar Shehun Borno da Sarkin Zazzau sun halarta, tare da shugabannin kungiyar JIBWIS da JNI
- Mahalarta taron sun tattauna kan hanyoyin kawar da matsalar rashin tsaro da inganta ilimi da kiwon lafiya a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya tara manyan sarakuna da malaman addini daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Sarkin Musulmi da kansa ya zama shugaban zaman, yana aiki a matsayin shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar shi ta Sultan.

Source: Facebook
Sahfin Daular Usmaniyya a kafar Facebook ya wallafa cewa an yi zaman ne a birnin Kaduna ranar Talata, domin muhimmin taro da Gidauniyar Sultan ta kira.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 da manyan sarakunan Arewa sun cimma matsaya kan kafa yan sandan jihohi
Malamai da Sarakuna sun hallara
Daga cikin sarakunan da suka isa Kaduna akwai Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli; Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi; Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.
Akwai Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu; Sarkin Argungu, Alhaji Sama'ila Muhammad Mera; da kuma Etsu Pategi, Alhaji Umaru Ishaq Bawa, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar sarakunan jihar Kwara.
Haka zalika malamai sun halarci taron, ciki har da shugaban JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau; Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi,
Sakataren Janar na JIBWIS, Sheikh Kabir Haruna Gombe; da kuma Sakataren Janar na Jama'atu Nasril Islam, Dr. Khalid Aliyu da wakilin Sheikh Jingir, Dr Hassan Dikko.
Abin da aka tattauna a taron
Bisa rahoton Daily Trust, mahalarta sun tattauna kan yadda za a karfafa hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin sarauta, shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki domin magance kalubalen rashin tsaro da ke addabar yankunan Arewa.
An kuma yi magana kan bunkasa ilimi, musamman ilimin 'yan mata, haka nan yadda za a inganta kiwon lafiya da tallafa wa marasa karfi.
Gidauniyar Sultan ta kasance tana aiwatar da shirye-shirye da dama masu amfani ga al'umma, wadanda suka hada da zaman lafiya da sulhu, horas da yara mata a makaranta, tallafi ga masu bukatar agaji da kuma yaki da karancin abinci.

Source: Facebook
Taron ya zo ne a wani lokaci da matsalar rashin tsaro ta ci gaba da addabar yankin Arewa, inda 'yan bindiga da sauran munanan abubuwa suke kawo cikas a yankin.
Halartar manyan sarakuna da malaman addini wannan taro ya nuna muhimmancin da waɗannan jagororin al'umma ke bayarwa wajen neman mafita ga matsalolin yankin.
Legit ta tattauna da Malam Usman
A tattauna wa da malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Ahmad, ya bayyana wa Legit cewa matakin da sarkin ya dauka yana da matukar muhimmanci.
Ya ce:
"Hakan da ya yi ya nuna cewa shi shugaba ne da zai jagoranci al'umma. Akwai bukatar a hada kan jama'a.
"Ya kamata kowa ya sani cewa akwai matsalolin da suke bukatar hadin kan kowa. Ta haka ne kawai za a magance su."
Sultan ya gana da 'yan Vatican
A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar II ya gana da tawagar Fafaroma Leo a Abuja.
A yayin ganawar da suka yi, Sarkin Musulmi ya sanar da cewa wajibi ne shugabannin addini su mayar da hankali wajen hada ka 'yan kasa.
Sultan ya yi gargadi da cewa yada labaran kanzon kurege na cikin abubuwan da ke kara ruruta rikici a tsakanin al'umma a wannan zamani.
Asali: Legit.ng

