Daga zuwa NDC, Babachir ya shiga tono abubuwa har da bayyana masu munafuntar jam'iyya

Daga zuwa NDC, Babachir ya shiga tono abubuwa har da bayyana masu munafuntar jam'iyya

  • Babachir David Lawal ya yi zargin cewa wasu ‘yan takarar gwamna a NDC na aiki ne domin karya Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
  • Ya bukaci magoya bayan NDC su yi watsi da abin da ya kira dabarun ‘yan jam’iyyar masu neman kawo cikas a Arewa maso gabas
  • Babachir ya ce Aisha Dahiru-Binani tana tare da Atiku Abubakar, amma ya wanke su Mohammed Sani Yahaya da Babayo Ardo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Adamawa - Babachir David Lawal ya fitar da jawabi na musamman bayan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar hamayya ta NDC.

Tsohon sakataren Gwamnatin tarayyar ya yi martani ne kan batun da ake cewa wasu ‘yan takarar gwamna a NDC ba su tare da shi.

Yan takaran NDC
Yan takaran NDC a zaben 2027, a fadar Sarkin Musulmi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Akwai masu adawa da Babachir Lawal a NDC

A shafinsa na Facebook, Sanata Babachir David Lawal ya nuna cewa Aishatu Dahiru-Binani ce ta shirya wannan lamari ba kowa ba.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur

Fitaccen ‘dan siyasar ya daura zargin a kan mace da ke takarar gwamna a Adamawa a karkashin jam’iyyar NDC a zabe mai zuwa.

Ana zargin cewa masu takarar gwamna a Arewa maso gabas ba su ji dadin yadda aka karbi Babachir, aka nada shi jagora a yankin ba.

Ya ce babu ruwan Farfesa Mohammed Sani Yahaya da Dr Babayo Ardo da suke neman zama gwamnoni a Taraba Gombe da tafiyar.

NDC ta nada Babachir jagora a jihohi 12

Babachir ya ce ba a sanar da shi a hukumance cewa ya zama jagoran NDC a jihohin Arewa maso gabas da na Arewa maso tsakiya ba.

A rubutun da ya yi a Facebook ranar Litinin, ya ce duk da bai nema ba, ya karbi wannan nauyi saboda ganin girman Seriake Dickson.

Baya ga haka ya ce yana ganin kimar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso kuma yana daraja su don haka ba zai iya cewa ba zai yi aikin ba.

Kara karanta wannan

Duk da yana jam’iyyar adawa, gwamna ya fadi abin da ya sa zai goyi bayan Tinubu

Babachir ya zargi wasu 'yan NDC da yaudara

"Na san cewa shigowa ta NDC za ta zama babbar barazana ga masu yi wa Atiku aiki a NDC, suna cin dunduniyar Peter/Kwankwaso.
"Mun gode wa Ubangiji da yanzu sun fara tona kansu kuma mutanen Arewa maso gabas sun gane."

- Babachir David Lawal

Injiniya Babachir ya zargi Aisha Binani da shiga takarar gan-gan yake cewa tafito neman gwamnan Adamawa ne kawai saboda kabilanci.

‘Dan siyasar ya ce tun farko bai yarda da ita ba ganin yadda ita ce ta saye kusan duka fam na masu neman takara a Adamawa a inuwar NDC.

Atiku zai sha kasa a Adamawa a hasashen Babachir

Kamar yadda ya fada, ya ziyarci mahaifar tasa tsakanin 25 ga Agusta zuwa 10 ga Satumban nan, amma babu wata alamar jam’iyyar NDC.

A sakamakon shigowarsa NDC, Babachir ya ce mafi yawan ‘yan takara musamman a Adamawa, Taraba, Gombe da Borno za su ci zabe.

Rubutun ya yi hasashen Atiku Abubakar zai kunyata a mahaifarsa a 2027 tunda ya fallasa shirin irinsu Binani da suke yin zagon-kasa.

Kara karanta wannan

Pantami: PDP ta shirya fitar da ɗan takarar gwamnan jihar Gombe tsakanin mutum 3

Gwamnan Abia ya fitar da Obi kunya

Gwamna Alex Otti ya sake jaddada cewa Peter Obi ya tara dala miliyan 155 a asusun Jihar Anambra kamar yadda labari ya zo a baya.

A lokacin da yake Shugaban Bankin Diamond, Otti ya ce shi da bakinsa ya shawarci Obi da ya canza kudin su zama dalolin kasar Amurka.

Yau gwamnatin Jihar Anambra tana zargin Obi da barin bashin $120m da ya karbo daga ketare, batn da ya kawo masa matsala a takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng