Illar da Yaki da Kasar Amurka Ya Jawo wa Iran Bangaren Tattalin Arziki

Illar da Yaki da Kasar Amurka Ya Jawo wa Iran Bangaren Tattalin Arziki

  • Darajar kuɗin Iran ta sake faduwa inda aka samu sama da rial miliyan 2.5 kan dalar Amurka a Tehran
  • Faduwar kuɗin ta zo ne kwanaki 27 bayan rial ya kai rial miliyan 2.2 kan dala a ranar 2 ga Satumba, yayin da ya ci gaba da yin baya
  • Ministan harkokin wajen Iran ya ce tattaunawar kai-tsaye da Amurka kan buɗe mashigar Hormuz ta ƙara tsananta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Darajar kuɗin Iran ta sake faduwa zuwa wani sabon matakin tarihi a ranar Talata, inda ’yan kasuwa a Tehran suka rika musayar rial sama da miliyan 2.5 kan dala.

Wannan faduwar darajar rial na nuni da yadda yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da raunana tattalin arzikin kasar Iran, wanda tuni yake fuskantar matsaloli.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Matsalar da ta faru a Iran yayin yaki da Amurka
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Yadda darajar kudin Iran ke faduwa

Sabuwar faduwar ta zo ne kwanaki 27 kacal bayan rial ya kai sabon ƙarancin tarihi na rial miliyan 2.2 kan dala a ranar 2 ga Satumba, cewar AP News.

Tun bayan fara yaƙin a watan Fabrairu, darajar kuɗin Iran ta ci gaba da faduwa a wani mataki na tarihi.

Tattalin arzikin Iran ya shafe shekaru yana fuskantar matsin lamba sakamakon takunkuman ƙasa da ƙasa da aka kakaba wa ƙasar.

Sai dai wani shingen jiragen ruwan Amurka kan man Iran da sababbin takunkuman da aka sanya tun bayan fara yaƙin, sun kara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mummunan hali.

A gefe guda, babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce tattaunawar kai-tsaye da Amurka kan sake buɗe mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci ta ƙara zama mai tsanani.

Haka kuma, babban kakakin Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, Janar Hossein Mohebbi, ya yi kira ga Amurkawa su fito kan tituna su yi zanga-zangar adawa da yaƙin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Yadda yakin Amurka ya taba kasar Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka yayin kamfen zaben zabe a New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Iran ta bayyana yiwuwar sabuwar tattaunawa

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya shaida wa kafafen yaɗa labaran Iran a ƙarshen ranar Litinin cewa abin da ake mayar da hankali a kai yanzu shi ne mashigar Hormuz.

Araghchi ya ce mashigar ita ce wurin da yaƙin ya fi karkata a halin yanzu, saboda muhimmancinta ga zirga-zirgar jiragen ruwa da makamashi.

Ya bayyana hakan ne jim kaɗan kafin ya bar birnin New York, inda ya halarci taron shugabannin duniya na Majalisar Ɗinkin Duniya a makon da ya gabata.

Ya kuma yi wannan bayani ne bayan ganawa da masu shiga tsakani daga Pakistan da Qatar, waɗanda ke ƙoƙarin taimakawa wajen warware rikicin.

Araghchi ya ce ana sa ran masu shiga tsakani daga Qatar za su sake tuntuɓar ɓangaren Amurka domin tattauna batun mashigar Hormuz, cewar News Times.

Iran ta sake yin barazana ga Amurka

Mun ba ku labarin cewa Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC ta yi barazanar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka hari idan Washington ta sake ƙaddamar da wani yaƙi da Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo babbar matsala bayan Iran ta mika tayin buɗe Hormuz ga Amurka

Wani babban jami’in IRGC ya ce Iran za ta iya kai hari kan jiragen Amurka har cikin Tekun Indiya idan sabon rikici ya ɓarke.

Barazanar ta zo ne yayin da rashin jituwar Iran da Amurka kan mashigin Hormuz ke ci gaba, duk da raguwar faɗan da ake yi a 'yan makonnin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.