CBN Ya Ware Mutane da Yan Kasuwar Jihar Kano, Ya Aika Masu da Sako kan Takardun Naira
- CBN ya bukaci ’yan kasuwa da mazauna Kano su rika kula da takardun Naira, tare da nuna masu illar rashin kula da takardun kudin Najeriya
- Babban bankin ya fara gangamin wayar da kai a manyan kasuwannin Kano domin karfafa wa jama’a gwiwar kula da Naira
- CBN ya ce kula da Naira zai taimaka wajen tsawaita tsawon rayuwar takardun kudi da rage kudin da ake kashe wa wajen sauya su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci ’yan kasuwa da sauran mazauna Jihar Kano su rika kula da takardun Naira a harkokinsu na yau da kullum.
Bankin ya bayyana cewa rashin kula da takardun kudin na jawo lalacewarsu, wanda ke tilasta wa gwamnati kashe makudan judi wajen sauya takardun da suka lalace ko suka baci.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa CBN ya yi wannan kiran n yayin da ya fara gangamin wayar da kai a manyan kasuwannin Kano domin karfafa wa ’yan kasuwa da sauran jama’a gwiwar rike Naira da mutunci.
CBN ya ja hankalin yan kasuwar Kano
Da yake magana yayin gangamin a Kasuwar Galadima, wakilin Sashen Kudi da Ayyuka na CBN, Ibrahim Yahya, ya ce Naira alama ce ta ’yancin kan Najeriya da kuma alfaharin kasa, don haka ya kamata a rika kula da ita yadda ya kamata.
Yahya ya ce CBN da Gwamnatin Tarayya na kashe makudan kudade wajen sauya takardun kudi da suke zama datti, lalatattu ko suka yage saboda rashin kula da su.
“Ta hanyar kula da Naira yadda ya kamata, muna tsawaita tsawon rayuwar kudin, sannan ta hakan muna tanadin makudan kudade da za a kashe wajen sauya wadanda suka lalace,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur
Dalilin fara wayar da kan yan kasuwa
Ya ce CBN ya zabi kasuwanni a matsayin wurin fara gangamin ne saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen hada-hadar kudade, musamman a Kano, wadda ya bayyana a matsayin babbar cibiyar kasuwanci.
A cewarsa, ’yan kasuwa na karbar dimbin kudade daga kwastomomi tare da rike su kafin su kai wani bangare na kudaden da suka samu banki, lamarin da ya sanya su cikin masu ruwa da tsaki wajen kiyaye ingancin kudin kasa.
“Mun yi imanin cewa idan muka yi magana da ’yan kasuwar kansu, nan ne wurin farawa. Suna tara kudade, kuma watakila bayan sun yi amfani da wani bangare wajen hada-hadar kasuwancinsu, su kai sauran banki,” in ji shi.

Source: Getty Images
Yahya ya ce wayar da kan ba za ta tsaya a Kasuwar Galadima kadai ba, domin CBN na shirin kai sakon zuwa wasu manyan kasuwanni a fadin jihar, cewar rahoton Vanguard.
Kasuwannin da aka ware domin gangamin sun hada da Kasuwar Sabon Gari, Abattoir, Kasuwar Yankaba, Kasuwar Tarauni, Yan Lemo da Kasuwar Hatsi ta Dawanau.
Wakilin CBN ya bukaci ’yan kasuwa da sauran masu amfani da Naira su rika rike takardun kudin da “alfahari” da mutunci.
CBN ya musanta daina amfani da N100
Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa tsohuwar takardar kuɗin N100 tana nan a matsayin halastaccen kudi.
Babban bankin ya ce ya lura da rahotannin da ke cewa wasu mutane da 'yan kasuwa sun fara ƙin karɓar takardar N100 saboda shakku kan ingancinta.
Babban bankin ya bayyana cewa dole ne a karɓe ta wajen gudanar da duk wata mu'amalar kudi a faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng

