Yadda Motoci Suka Nutse, Komai Ya Tsaya Cak bayan Ambaliya a Abuja

Yadda Motoci Suka Nutse, Komai Ya Tsaya Cak bayan Ambaliya a Abuja

  • Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Abuja, inda ya katse zirga-zirga tare da tilasta wa wasu ‘yan kasuwa rufe shagunan su
  • Ambaliyar ta shafi titunan Wuse 2, Gudu da Lokogoma, yayin da gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi ta cika da ruwa lamarin da ya tilastawa koya ya tsaya cak
  • Sama da Naira biliyan 109.5 aka fitar daga Asusun Kula da Muhalli na Najeriya tsakanin Yuli 2023 da Disamba 2025 domin tunkarar matsalolin muhalli a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja – Ruwan sama mai ƙarfi ya kawo cikas ga zirga-zirga a sassa daban-daban na Abuja a ranar Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026.

Wannan ya biyo bayan ambaliya da ta mamaye manyan tituna da wasu unguwanni, lamarin da ya sa wasu masu ababen hawa suka makale, yayin da wasu ‘yan kasuwa suka rufe wuraren kasuwancinsu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitin mu da Peter Obi a 2027'

An samu ambaliya a wasu sassan Abuja
Ambaliya ta shafe wasu yankuna a duniya Hoto: STR
Source: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin wuraren da ambaliyar ta yi kamari akwai Adetokunbo Ademola Crescent da ke Wuse 2, yankin da ke kusa da Delight Event Centre a Gudu, da wasu sassan Efab Estate da ke Lokogoma.

Yadda ambaliya ta hana komai a Abuja

Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa ambaliyar ta mamaye gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi, lamarin da ya hana masu ababen hawa ketare ta yadda ya kamata.

Wasu motoci sun nutse cikin ruwa ko kuma suka samu matsala sakamakon tashin ruwan, yayin da wasu ‘yan kasuwa a wuraren da abin ya shafa suka rufe wuraren kasuwancinsu saboda ruwa ya fara shiga harabar su.

Wani mazaunin Abuja da ya ɗauki bidiyon halin da ake ciki a titin Ebeano-Gudu ya yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, da ya gaggauta ɗaukar mataki domin magance matsalar ambaliyar.

Kiran Mazauna Abuja ga ga Wike

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan matatun mai bayan karɓar tawagar NUPENG

Mutumin da ya yi magana ya ce mutanen da ke zuwa daga mahadar Gudu ba za su iya wucewa ba, haka mutanen da ke zuwa daga Ebeano ba za su iya zuwa Gudu ba.

Jama'a sun nemi agajin Wike a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Ya ce:

“Ya Mai Girma Ministan FCT, don Allah ku kawo mana agaji. Wannan shi ne halin da titin Ebeano/Gudu yake ciki a yanzu. Gadar ta cika da ruwa."

Ambaliyar ta katse zirga-zirga tsakanin Ebeano da Gudu, inda masu ababen hawa da mazauna yankin suka koma amfani da wasu hanyoyi yayin da ruwa ya mamaye titin da gadar da ke haɗa wuraren.

Ambaliya za ta yi barna

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NiMet ta gargadi jihohi 20 game da yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025, inda Sokoto ke cikin matsanancin haɗarin ambaliyar.

Hukumar ta lissafa Kaduna, Zamfara, Yobe, da sauran jihohi 16 a matsayin jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin watan Yuli na shekarar 2026 yayin da damina ta kankama.

NiMet ta ba da shawarwari kan tsaftace magudanan ruwa, guje wa tuki yayin da ake ruwa, da yin kaura daga wuraren da ambaliya za ta shafa domin a dauki matakan kariya da rigakafi daga ambaliyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng