A Kokarin Sace Shugaban Karamar Hukuma, Mutane Fiye da 70 Sun Fada Tarkon Yan Bindiga
- An sace akalla mutane 75 a sababbin hare-haren da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Bungudu da wasu kauyuka a Zamfara
- Maharan sun kashe mutum guda tare da sace wasu 13 a kusa da gidan shugaban karamar hukumar Bungudu
- An kuma sace mutane 44 a Magama Mai Rake, yayin da aka kai hari Yargada da Maikogo inda aka sace wasu mazauna 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Akalla mutane 75 ne aka sace a sababbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Karamar Hukumar Bungudu da wasu kauyuka uku da ke karkashin Gundumar Magami a kananan hukumomin Gusau da Maru na Jihar Zamfara.
Wani mazaunin garin Bungudu mai suna Abdurrazaq ya ce ana zargin ’yan bindigar sun kai harin ne domin sake sace shugaban Karamar Hukumar Bungudu, wanda ya tsere daga maboyarsu kwanan nan.

Source: Original
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hare-haren sun faru ne a yammacin ranar Lahadi da kuma farkon safiyar Litinin da ta gabata.
Yan bindiga sun dawo wurin ciyaman
Kansilan Mazabar Bungudu a Karamar Hukumar Bungudu, Honarabul Anas Sulaiman, ya ce ’yan bindigar sun zo da yawa, inda suka sace kusan mutane 13 a kusa da gidan ciyaman, suka kashe mutum guda sannan suka tafi da mutane.
“A fili yake cewa shugaban karamar hukumar ne suka zo nema,” in ji shi.
Ya ce ’yan bindigar sun kai hari hedikwatar karamar hukumar ne a yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutum guda tare da sace wadanda abin ya shafa.
An sace mata da yara a Zamfara
A wani makamancin wannan lamari, ana zargin ’yan bindiga sun mamaye garin Magama Mai Rake da ke Karamar Hukumar Maru da misalin karfe 12 na dare ranar Litinin, inda suka bude wuta kafin su fara binciken gidaje daya bayan daya.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun bi dare, sun kama tare da kashe sakataren harkokin lafiya a Katsina
Wani wanda ya tsira daga harin, Malam Lawali Kutsa Ada, ya shaida cewa maharan sun sace kusan mutane 44, mafi yawansu mata da yara, sannan suka kona motoci kusan 10.
Wani shaidar gani da ido, wanda ya nemi a boye sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce ’yan sanda sun kawo dauki bayan samun kiran gaggawa, amma ba su iya tunkarar ’yan bindigan ba saboda yawansu da kuma karfin makamansu.
A lokaci guda, maharan sun kuma kai hari kauyukan Yargada da Maikogo, wadanda dukansu ke karkashin Gundumar Magami ta Karamar Hukumar Gusau, inda suka sace mutane 20.
’Yan sanda sun fara aikin ceto
Da yake tabbatar da hare-haren, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce rundunar ta samu rahoton sace mutane a Bungudu kuma ta tura tawaga domin ceto su.

Source: Getty Images
Abubakar ya kara da cewa an kuma tura tawagar zuwa Magama Mai Rake da ke Karamar Hukumar Maru domin tabbatar da sakin wadanda aka sace.
Ya ce rundunar tana ci gaba da bincike domin gano hakikanin adadin mutanen da aka sace, yana mai cewa adadin na iya zama kasa da wanda al’ummomin yankunan suka bayyana.
Yadda ciyaman na Bungudu ya kubuta
Kun ji cewa an ceto shugaban karamar hukumar Bungudu, Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane 4 da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda a jihar Zamfara.
Rundunar sojoji ta ce mutanen sun tsere ne a yankin Karamar Hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, inda daga bisani sojoji suka shiga daji suka dauko su.
Asali: Legit.ng

