Kungiyar Kirisrocin Najeriya CAN
Babban malamin nan, Emeritus Archbishop na Abuja ya bukacu shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yan Najeriya aiki ba tare da nuna fifiko ba.
Babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya ce Najeriya ta samu taimakon Allah shiyasa canjin Dala bai kai N10,000 ba yanzu, ya faɗi mafitar da ta rage.
Cocin RCCG ta bayyana dakatar da wasu fastoci biyu bayan zarge-zargen luwadi sun yi yawa a kansu, ta sa a gudanar da bincike mai zurfi nan da makonni biyu.
Wani limamin cocin katolika, Rabaran Tsomas ya nuna halin dattako, inda ya mika kansa ga ƴan bindiga domin su saki ɗalibai 2 da suka yi garkuwa da su a Edo.
Shugaban cocin INRI, Primate Elijah Ayodele ya soki garambawul da Shugaba Tinubu ya yi a majalisar ministocin kasar nan, inda ya ce ba wadanda ya kamata aka kora ba.
Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa a bara ta rufe wasu masallatai, coci-coci da wurare daban-daban 352 saboda karya dokar ɗaga sauti a faɗin jihar.
Kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi Allah wadai da saka haraji kan allunan coci. CAN ta ce bai kamata a saka haraji a kan wuraren ibada ba kuma gwamnan Abia ne ya fara.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bukaci malaman kasar nan da su kasance masu fadawa shugabanni gaskiya amma su daina zaginsu.
Primate Elijah Babatunde Ayodele ya hango cewa za a iya fuskantar karamar girgizar kasa a jihar Legas nan ba da jimawa ba. Ya nemi mutane su dage da addu'a.
Kungiyar Kirisrocin Najeriya CAN
Samu kari