Matashin da Ya Yi Rai Ya Bada Labarin Yadda Mutane 37 Suka Mutu hannun NSCDC a Minna
- Masu rai suna ta bada labarin abin da ya faru da jami'an NSCDC suka kama masu hakar ma’adanai a jihar Neja
- Wani da ya sha da kyar, ya yi zargin cewa an yi masu feshin wani sinadari mai kamshi amma wanda yake d guba
- Bayan feshin ne mutane suka rika mutuwa, yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’ai kuma ana bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Adamu Isa mai shekara 19 ya tashi ranar 17 ga Satumba 2026 kamar kullum, amma bai san bala’in da yake jiransa ba.
A ranar ne Adamu Isah ya kare a dakin jami’an hukumar NSCDC a garin Minna, lamarin da ya yi sanadiyyar ajalin wasu.

Source: Getty Images
Labarin mai harkar ma'adanai da ya yi rai
Wani zungureren rahoto na Premium Times ya kawo labarin abubuwan da wannan bawan Allah ya gani da jami’ai suka kama su.
Har yanzu akwai tabon cizo biyu a jikin Adamu Isah sakamakon dankara masa hakori da wani ya yi a lokacin da yake gargarar mutuwa.
Wannan bawan Allah yana cikin wadanda jami’an NSCDC suka kama saboda suna hakar ma’adanai a yankin Wushishi/Lukoto a Neja.
Da yake magana da jaridar, ya bayyana abubuwan da suka faru tun lokaci da aka kama su har zuwa rasuwar wasu abokan aikinsa 37.
Ranar da aka kama masu hakar ma'adanai
Ya ce an yi ram da su ne a wajen M.I. Wushishi suna shirin fita aiki, daga nan kuma sai aka tafi da su zuwa wurin da aka tsare su.
Dakin tsaron yana kusa da sakatariyar jam’iyyar PDP a garin Minna. Kuma an fara ne da kai mutane 20 amma sai aka bada belinsu.
"Bayan kwanaki biyu a nan, sai aka bada belin kusan mutane 20. Sai aka bar mu 17 a dakin."

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun bi dare, sun kama tare da kashe sakataren harkokin lafiya a Katsina
- Adamu Isah
Jami'an NSCDC sun fesa abu kamar turare
Da mutane suka karu, sai aka rika raba wadanda aka kama zuwa wasu ‘yan kananan dakuna na mata da maza masu cike da cunkoso.
Ana fama da rashin iska da kazanta, sai a rana ta uku Malam Adamu Isa ya ce jami’an suka fesa masu wani sinadari mai kanshin turare.
Adamu yake cewa:
“Yana kanshi kamar turare, amma yana da danshi da lema, saboda haka mun sa ba turaren da aka sani ba ne,”
Matashin ya ce daga nan sai ‘yan cikin dakin suka rika neman wurin da za su shaki iska, bayan awa guda kenan sai sinadarin ya fara aiki.
Ana cikin haka ne ya ce wani bagwari ya fara nishi, yana fitar da wani abu mai kumfa daga bakinsa, sanadiyyar mutuwarsa kenan suna gani.
Ya ce:
“Daga nan mutane suka fara mutuwa”

Source: Getty Images
Ma'aikatan NSCDC sun ce masu su mutu
Kafin su mutu, wasu sun rika buge-buge, aka samu masu cizo da masu dukan kai a bango, suka rika yin abubuwa tamkar mahaukata.
Da suke ihu, suka roki jami’an tsaron su fito da su, a cewarsa, sai aka ce su je can su duk su mutu.
Kamar yadda ya fada, su 17 sun iya fitowa amma mutane 11 kadai aka iya ruga wa da su zuwa asibiti domin a ba su agajin gaggawa.
Har zuwa lokacin da yake magana, Adamu Isah ya ce bai gama samu cikakkiyar lafiya ba.
Atiku ya yi ta'aziyyar rasuwar masu hakar ma'adanai
Ana da labari Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci Minna a Jihar Neja domin yi wa Sarkin Minna da iyalan masu haƙar ma'adanai ta'aziyya.
Ya ba da tallafin ₦20m ga iyalan mutane 37 da suka mutu a hannun jami'an NSCDC sakamakon mawuyacin halin da aka jefa su.
Atiku ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba manufofinta na tattalin arziki domin rage tsadar rayuwa kuma a ba matasa ayyukan yi.
Asali: Legit.ng

