
Addinin Musulunci da Kiristanci







Malaman cocin Katolika sun bukaci gwamnati da ta mayar da hankali kan rage wahalar tattalin arziki da samar da tsaro don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kai ziyara domin yin ta'azziya ga gwamnan Filato, Caleb Mutfwang bayan rasuwar Sheikh Sa'id Hassan Jingir.

Gwamna Soludo ya haramta wa’azi a kasuwannin jihar Anambra, yana mai cewa yana haddasa hayaniya. Shugabannin addini sun ce hakan cin zarafin ‘yancin addini ne.

Gwamnatin jihar Anambra ta haramta wa’azi da lasifika musamman a kasuwanni tana mai cewa hayaniya na hana mutane sukuni inda ta ce babu dole a yin addini.

Yayin da aka shiga watan azumin Ramadan akwai wasu hanyoyi da mutum zai bi domin sauke Alkur'ani mai girma a cikin kwanaki 30 kacal a watan azumi.

Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh ya yi buda baki da Musulmai a masallaci inda ya bukaci zaman lafiya tsakanin addinai yayin ziyararsa a masallacin Al-Habibiyya.

Yayin da ake maganganu kan rufe makarantu a Ramadan, Majalisar shari’ar Musulunci ta goyi bayan matakin a Ramadan, tana cewa hakan zai taimaka wa dalibai.

Kungiyar CAN ta gargadi wasu gwamnonin Arewacin Najeriya guda hudu kan rufe makarantu saboda samun sauki a azumin watan Ramdan da ake ciki a yanzu.

Rabaran Matthew Kukah ya ce mutane 12,000 sun mutu a Arewa maso Yamma cikin shekaru 10, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda. AAn kawo hanyoyin dakile rikicin.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari