Sultan Ya Bukaci Dukkan Musulman Najeriya Su Fita Duba Watan Safar a Yau

Sultan Ya Bukaci Dukkan Musulman Najeriya Su Fita Duba Watan Safar a Yau

  • Majalisar Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwa fara duba jinjirin watan Safar na shekarar 1448AH a ranar Talata, 14 ga Yulin 2026
  • •Wanda ya ga watan zai kai rahoto ga hakimin yankinsa domin ya kai wa sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar labari
  • Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya rattaba hannu kan sanarwar a matsayinsa na shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa ranar Litinin yana kiran dukkan Musulmin Najeriya su yi shirin neman jinjirin watan Safar na shekarar 1448.

Bisa sanarwar da aka fitar, ranar Talata, 14 ga Yuli 2026, wadda ta yi daidai da rana ta 29 ta watan Muharram 1448AH, ita ce rana da Musulmi za su duba sararin sama don neman sabon wata.

Kara karanta wannan

Tofa: Shugaban wata hukuma a Abuja ya ƙi barin ofis duk da Tinubu ya sauya shi

Sarkin Musulmi da hoton wata
Mai alfarma Sarkin Musulmi a hagu, wata a dama. Hoto: JNI|Getty Images
Source: UGC

Sahafin Sarkin Musulmi ya wallafa a Facebook cewa Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya rattaba hannu kan sanarwar da aka fitar.

Maganar duba wata a Najeriya

Majalisar Masarautar Sakkwato ta buƙaci al'ummar Musulmi a faɗin Najeriya da su fara neman jinjirin watan Safar 1448AH a ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Muharram 1448AH.

A cewar sanarwar, duk Musulmin da suka ga jinjirin watan ana roƙonsu da su gaggauta kai rahoton ganinsa ga hakimi ko shugaban ƙauyensu mafi kusa, domin a isar da shi ga mai alfarma Sarkin Musulmi.

Sanarwar ta ce:

“Wannan sanarwa ce ga al'ummar Musulmi cewa ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga watan Muharram 1448AH, ita ce ranar neman jinjirin watan Safar 1448AH.”

Kira a fita duba wata

Punch ta wallafa cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci al'ummar kasar da su fita duba wata a dukkaan sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Barau Jibrin ya fadi amfanin shirin ga Arewacin Najeriya

Ya ce:

“Saboda haka, ana roƙon Musulmi da su fara neman ganin jinjirin watan Safar 1448AH a ranar Talata, sannan duk wanda ya gan shi ya kai rahoto ga Hakimi ko shugaban ƙauyensa mafi kusa domin a isar da shi ga Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).”

Majalisar ta jaddada cewa neman ganin jinjirin wata wata muhimmiyar ibada ce a Musulunci, wanda ake amfani da shi wajen tabbatar da shiga sabon watan Musulunci.

Sarkin Musulmi a wajen taro
Mai alfarma Sarkin Musulmi yana jawabi. Hoto: JNI
Source: Twitter

Addu'a da fatan alheri

Farfesa Junaidu ya yi addu’ar Allah Ya ba da ikon gudanar da wannan ibada yadda ya kamata kuma Ya karɓa, inda ya ce:

“Allah Maɗaukakin Sarki Ya taimake mu wajen sauke wannan nauyi. Amin.”

Kiran Sultan kan rashin tsaro

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma sarkin Musulmi ya yi kira ga shugabannin Arewa da su hada kai wajen yaki da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka da ke zuga Trump kan yaƙar Iran da sauran manufofin kasar ya rasu

Sarkin ya yi magana ne yayin da gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya da sarakunan gargajiya suka hadu a Kaduna domin tattauna matsalolin yankin.

A bayanin da ya yi, Sultan ya bayyana cewa babu yadda za a yi nasara a yaki da ta'addanci ba tare da manyan Arewa sun hada kai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng