Tinubu zai Hallara Taron Izala da Kungiyar Musulmin Duniya za Su Yi

Tinubu zai Hallara Taron Izala da Kungiyar Musulmin Duniya za Su Yi

  • Shugaba Bola Tinubu zai buɗe taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da haɗin kan ƙasa da JIBWIS ta shirya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Musulmi ta Duniya ta Saudiyya
  • Taron na kwanaki biyu zai mayar da hankali kan matsalolin satar mutane, 'yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro da ke addabar Najeriya
  • Za a gudanar da taron ne a Abuja, inda malamai, masana tsaro, sarakunan gargajiya da masu tsara manufofi daga Najeriya da ƙasashen waje za su halarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai buɗe wani taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da haɗin kan ƙasa da Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Musulmi ta Duniya ta Saudiyya.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Za a sake kai korafi gaban Trump kan kashe kashe a Arewa

Taken taron shi ne batun zaman lafiya tsakanin al’umma, kuma zai haɗa malamai, masu tsara manufofi, masana tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga Najeriya da ƙasashen waje.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu yana wani bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Puch ta rahoto cewa za a gudanar da taron na kwanaki biyu ne a Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, daga ƙarfe 9 na safe ranar Talata, 11 ga Agusta.

Makasudin taron Izala a Abuja

Masu shirya taron sun ce an shirya shi ne domin tattauna matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a cikin mahallin duniya, tare da duba yadda haɗin gwiwar addini da zaman lafiya tsakanin al'umma za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.

Za a tattauna batutuwan satar mutane, ayyukan 'yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da barazana ga rayukan 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Masu shirya taron sun ce matsalolin satar mutane da 'yan bindiga sun zama wasu daga cikin manyan barazanar tsaron ƙasar, don haka akwai buƙatar samar da hanyoyin magance su ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati, malamai da al'umma.

Kira ga haɗin kan Musulmi

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

Taron zai kuma tattauna rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar Musulmi, musamman bambance-bambancen mazhaba, ƙabila da asali, tare da neman hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya tsakanin Musulmi da mabiyan sauran addinai.

Masu shirya taron sun ce Musulmi za su iya riƙe mabambantan mazhabobinsu ba tare da mayar da bambance-bambancen zuwa tushen ƙiyayya da faɗa ba.

Sun ce:

“Ko da kuwa mutum ɗan wata ƙabila ce, Musulmi dole ne su ɗauki junansu a matsayin 'yan uwa a Musulunci. Babu zagi, babu kalaman tayar da hankali.”
Shugaban Izala a wajen taro
Sheikh Abdullahi Bala Lau a wajen taro. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Sarkin Musulmi zai halarci taron

Ana sa ran Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, zai kasance Babban Uban Taron, yayin da gwamnoni, ministoci, 'yan majalisun tarayya da jihohi, malaman addinin Musulunci da sarakunan gargajiya za su halarta.

Haka kuma, ana sa ran 'yan kasuwa da sauran mambobin al'ummar Musulmi daga Najeriya da wasu ƙasashe za su halarci taron.

Masana za su gudanar da wasu zaman musamman domin tattauna hanyoyin yaƙi da ta'addanci da ayyukan 'yan bindiga masu ɗauke da makamai.

Tinubu na zuwa ofis da kafa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga ta Najeriya, Zacch Adedeji, ya yi watsi da zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na almubazzaranci.

Kara karanta wannan

Matasa za su warwasa, an buɗe damar tallafa wa mutane 50,000 a jihohin Najeriya

Adedeji ya ce Tinubu kan yi tafiya da ƙafa daga gidansa zuwa ofis, kuma yana amfani da mota ne kawai idan zai je filin jirgin sama.

Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasar yana cin abinci sau ɗaya a rana, sannan bai fita daga Najeriya ba cikin watanni uku da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng