2027: Abin da Babban Jami'in Birtaniya Ya Tattauna da Atiku a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya gana da babban jami'in diflomasiyyar Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery
- Tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da ake ciki a Najeriya a halin yanzu, kamar yadda dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 ya bayyana
- Ganawar ta zo ne yayin da Birtaniya ke kara tuntubar shugabannin siyasa da jami'an zabe gabanin babban zaben 2027 da ake dab da gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, na ci gaba da ganawa da manyan baki gabanin 2027.
A wannan karon ya karbi bakuncin babban jami'in diflomasiyyar Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, da wasu manyan jami'an diflomasiyyar kasar.

Source: Facebook
Atiku Abubakar ya tabbatar da tattaunawar ta cikin sakonnin da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta da suka hada da Facebook a ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, 2026.
Atiku ya gana da jami'in Birtaniya
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewar Atiku, ya gana da Montgomery, shugaban sashen siyasa na ofishin diflomasiyyar Birtaniya, Lucy Green, da sakataren siyasa na biyu, Thomas Simpson.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan al'amuran da suka shafi Najeriya a halin yanzu, sai dai bai bayyana karin bayani kan abubuwan da aka tattauna ba ko kuma wurin da aka gudanar da ganawar.
Rahoton ya ce ganawar ta Atiku da jami'an Birtaniya ta zo ne a daidai lokacin da Babban Ofishin Birtaniya a Najeriya ke gudanar da ganawa da shugabannin siyasa da jami'an hukumar zabe gabanin babban zaben 2027.
Birtaniya na kara tuntubar 'yan siyasa
A watan Afrilun 2026, Babban Ofishin Birtaniya a Najeriya ya bayyana cewa Montgomery da mataimakinsa, Gill Lever, sun gana da wasu shugabannin siyasa da jami'an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC.
Ofishin ya ce yana fatan yin aiki tare da dukkan jam'iyyun siyasa domin taimakawa wajen gudanar da zabe mai cike da kowa kuma sahihi wanda kowa zaai gamsu.
Jami'an Birtaniyan sun kuma gana da mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku da Peter Obi, baya ga shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.
Rahoto ya tabbatar da zargin Atiku
A baya, mun kawo labarin cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce wani rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da korafe-korafen da ya yi kan gwamnatin Bola Tonubu.
Rahoton ya nuna damuwa kan rashin cikakken bayani kan kudaden shiga da kashe-kashen da gwamnatin Najeriya ta yi a bara wanda ya kunshi abubuwan da suka ja hankalin jama'a matuka.
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin yadda ake tara da kashe kudaden gwamnati tare da yi masu bayani dalla-dalla game da batutuwan da ba a gamsu da su ba.
Asali: Legit.ng

