Bayan Darika, Izala Ta Fadi Dan Takarar Gwamnan da za Ta Zaba a Kano a 2027

Bayan Darika, Izala Ta Fadi Dan Takarar Gwamnan da za Ta Zaba a Kano a 2027

  • Kungiar Izala a jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga takarar wa'adi na biyu da gwamna Abba Kabir Yusuf zai nema a zaben 2027
  • Shugaban kungiyar ya ce ayyukan raya kasa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi sun cancanci a ci gaba da su domin kawo cigaba a jihar
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi godiya ga kungiyar tare da jaddada kudirinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin inganta rayuwar Kanawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Reshen kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Kano ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar Izala ta bayyana cewa gwamnatin Abba ta karfafa jama'a, ta hanzarta kawo ci gaba, tare da daura jihar kan turbar samun ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

'Ban taba neman alfarma wajen ka ba': Sanusi II ya fadi buƙatarsu ga Abba Kabir

Abba Kabir Yusuf da Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a hagu, Abba Kabir Yusuf a dama. Hoto: Sanusi Bature -Tofa|Abdullahi Suraj Nagegime
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook a ranar Asabar.

Izala za ta zabi Abba a 2027

Shugaban JIBWIS na Jihar Kano, Farfesa Abdullahi Saleh, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidansa yayin ziyarar ta'aziyyar rasuwar matarsa.

Malamin ya yaba wa gwamnan bisa jagorantar ziyarar da kansa, yana mai cewa hakan alama ce ta tausayi, tawali'u da kuma girmama malamai a jihar.

Ya ce nasarorin da gwamnatin ta samu sun dawo da amincewar jama'a ga shugabanci, tare da mayar da Kano abin koyi wajen shugabanci mai manufa da kula da bukatun al'umma.

A cewarsa, ayyukan ci gaban da gwamnatin Gwamna Yusuf ta fara suna bukatar ci gaba domin a cika burin da aka sanya wa jihar na dogon lokaci.

Saboda haka, Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana goyon bayan JIBWIS ta Kano ga takarar wa'adi na biyu ta Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Tijjaniyya sun ajiye dan takarar Kwankwaso a gefe, sun bi Abba

Martanin Abba Kabir Yusuf

Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Farfesa Abdullahi Saleh bisa addu'o'insa, karfafa gwiwa da kuma amincewa da manufofin ci gaban gwamnatinsa.

Gwamnan ya kuma sake mika ta'aziyyarsa kan rasuwar matar malamin, tare da addu'ar Allah Ya gafarta mata, Ya jikanta da rahamarsa, Ya sanya ta Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.

Haka kuma, ya yaba wa malaman addinin Musulunci a Kano saboda kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, fahimtar juna da kuma tarbiyya a tsakanin al'umma.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da cibiyoyin addini, kungiyoyin Musulunci da shugabannin addinai domin kare kyawawan dabi'u da al'adun Kano, tare da inganta zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Darika ta goyi bayan Abba a 2027

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugabannin kwamitin shura na Darikar Tijjaniyya na jihar Kano ya nuna goyon baya ga tazarcen Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Hakan na zuwa ne bayan wani taron zikirin shekara-shekara da suka gudanar a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II a jihar Kano.

Kwamitin shurarar ya bayyana cewa gwamnan ya kawo cigaba sosai a shekarun da ya yi yana mulki saboda haka suke goyon bayan shi a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng