An Cafke Matashi Mai Tsaron Dazuka da Tinubu Ya Dauka da Alaka da Yan Bindiga

An Cafke Matashi Mai Tsaron Dazuka da Tinubu Ya Dauka da Alaka da Yan Bindiga

  • Jami’an tsaro sun kama wani sabon ɗan koyon aikin tsaron daji, Zahraddin Abdullahi Karadua, bisa zargin kai wa ’yan bindiga alburusai a Matazu, Katsina
  • A wani bidiyo, Zahraddin ya bayyana cewa wani mutum mai suna Muhammadu ya ba shi alburusai a Kano, ya kai su Karadua, sannan ya miƙa wa Sahiba
  • Sahiba ta amsa karɓar alburusai, inda ake zargin ta kai su wani sansanin ’yan bindiga da ake zargin yana kusa da ƙauyen Maharba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Jami’an tsaro sun kama wani matashi da ke daya daga cikin masu tsaron dazuka da gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen ayyukan ta'addanci.

An kama matashin ne mai suna Zahraddin Abdullahi Karadua, bisa zargin kai wa ’yan bindiga alburusai a ƙaramar hukumar Matazu ta Katsina.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi dare, sun kama tare da kashe sakataren harkokin lafiya a Katsina

An cafke matash da ke taimakawa yan bindiga
Hafsan tsaro a Najeriya, da matashi da aka cafke yana taimakawa yan bindiga a Katsina. Hoto: @DanKatsina50.
Source: Twitter

A wani bidiyo da shafin Bakatsina ya wallafa a shafin X, an ga Zahraddin ana yi masa tambayoyi bayan nasarar cafke shi da aka yi.

Yan bindiga sun yi barna a Katsina

Cafke matashin na zuwa ne yayin da wasu yan bindiga suka kai barna a jihar Katsina duk da ikirarin jami'an tsaro na cewa suna samun galaba a yaki da yan ta'adda.

A kwanakin nan, yan bindiga sun yi garkuwa da Sakataren Lafiya na Karamar Hukumar Malumfashi, Sa’adu Dantutture, tare da kashe shi a garinsu na Dantutture.

Rahoto ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe jami'in gwamnatin ne yayin wani hari da suka kai kauyen a daren Laraba.

An binne marigayin a garinsu yayin da iyalansa, abokan aikinsa, abokansa da mazauna yankin suka shiga jimami da addu’o’i.

Jami'an tsaro sun kama matashi kan tallafa wa yan bindiga
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalar yan ta'adda. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda matashi ke taimaka wa yan bindiga

Matashin ya bayyana yadda ya karɓi alburusai daga wani mutum mai suna Muhammadu a Kano, ya kai su Karadua, sannan ya miƙa wa wata mata mai suna Sahiba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Rahotanni sun ce Sahiba ta amsa cewa ta karɓi alburusai, inda ake zargin ta bayyana cewa daga baya ta kai su wani sansanin ’yan bindiga da ake zargin yana kusa da ƙauyen Maharba.

Wannan lamari ya haifar da muhimmiyar tambaya kan irin gudunmawar da fararen hula ke bayarwa da gangan wajen ci gaba da ayyukan ’yan bindiga.

Majiyoyi sun ce matashin na samar masu da alburusai, bayanai ko wasu nau’o’in tallafi ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka wanda ke kara jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

An yaye masu tsaron dazuka a Najeriya

An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yaye sama da jami’an tsaron dazuka 7,000 domin ci gaba da yaki da ta'addanci a Najeriya wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Jami'an da aka yaye sun fito ne daga jihohi bakwai domin dakile ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda.

Nuhu Ribadu ya tabbatar da fara tura jami’an aiki nan take, tare da fara biyansu albashi domin ƙarfafa tsaron cikin gida da kuma kara taimaka wa jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.