Hutu Ya Kare: Shugaba Tinubu Ya Bar Birnin Paris, ba Zai Sauka Abuja ba idan Ya Dawo Najeriya

Hutu Ya Kare: Shugaba Tinubu Ya Bar Birnin Paris, ba Zai Sauka Abuja ba idan Ya Dawo Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen hutun aikinsa a Turai kuma ya bar birnin Paris na Faransa domin komawa Najeriya
  • Tinubu zai fara sauka a Legas, inda zai karrama marigayi MKO Abiola tare da halartar bikin nuna wani fim da ke girmama rayuwarsa
  • Shugaban zai gudanar da wasu tarurrukan siyasa a Legas kafin ya koma Abuja, yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara kankama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo ƙarshen hutun aikinsa, inda ya bar birnin Paris na Faransa domin komawa Najeriya.

Ana sa ran jirgin Shugaba Tinubu zai sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a yammacin yau Talata, 29 ga watan Satumban 2026.

Tinubu zai dawo Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na dago hannu daga jirgin sama Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu zai fara sauka a Legas

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya duro Najeriya yayin da ake jiran dawowar Tinubu

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya zaɓi komawa Najeriya ta Legass ne domin karrama tarihin marigayi Cif MKO Abiola, wanda ake girmamawa a matsayin gwarzon gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya.

A Ranar ’Yancin Najeriya, shugaban zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim da aka shirya domin karrama Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na watan Yuni 1993.

Zai gana da ’yan siyasa a Legas

Yayin da yake Legas, Shugaba Tinubu zai gudanar da wasu muhimman tarurruka da shugabannin siyasa da abokan hulɗarsa na siyasa.

Ana sa ran tarurrukan za su gudana na wasu kwanaki, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.

Bayan kammala harkokinsa na siyasa a Legas, shugaban kasar zai koma babban birnin tarayya Abuja.

Tinubu ya shafe mako guda a Landan

Shugaba Tinubu ya bar Abuja ranar 30 ga Agusta domin fara hutun aikinsa.

Ya shafe mako guda a Landan kafin ya wuce Paris, inda ya ci gaba da zaman hutunsa tare da gudanar da wasu ayyukan da suka shafi ƙasa.

Kara karanta wannan

An samu sauyi a dawowar Tinubu, majiyoyi sun sanar da sabon lokacin dawowarsa

A Paris, ya halarci wata liyafar cin abinci ta sirri tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.

Ya kuma gana da wasu manyan ’yan kasuwa, ciki har da Vincent Bolloré na Bolloré Group, kamfanin da ke da harkoki a fannonin kafafen yaɗa labarai da fasahar dijital, ciki har da Canal+, MultiChoice da Universal Music Group.

A ranar Litinin kuma, Tinubu ya gana da Shugaban First Holdings, Femi Otedola.

Ya halarci rattaba hannu kan yarjejeniyar tashar ruwa

A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Gwamnatin Jihar Ogun da kamfanin DP World.

Yarjejeniyar ta shafi gina tashar ruwa mai zurfi ta Gateway a Ogun Waterside da kuma samar da Blue Marine Economic Zone a yankin.

DP World, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin gudanar da tashoshin jiragen ruwa da harkokin sufuri a duniya, na shirin zuba jarin dala biliyan 7 wajen aikin tashar ruwan da yankin tattalin arzikin.

Shugaba Tiubu zai dawo Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

An kai karar Tinubu gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar AAC ta kai Shugaba Bola Tinubu, Majalisar Tarayya da Antoni-Janar na Tarayya (AGF) gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Jam'iyyar AAC ta kai karar ne kan zargin cewa shugaban ƙasar bai sanar da Majalisar Tarayya ba kafin tafiya hutun wata guda a Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng