Duk da Yi Masu Gorin Tikitin Muslim Muslim, Kiristoci Sun Shirya Abin Alheri ga Tinubu

Duk da Yi Masu Gorin Tikitin Muslim Muslim, Kiristoci Sun Shirya Abin Alheri ga Tinubu

  • Shugabannin Kiristoci sun yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabanni addu’ar samun hikima
  • Fasto JohnPraise Daniel ya ce Najeriya za ta farfado duk da matsalolin ta’addanci, zubar da jini da matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta
  • Shugaban CAN ya bukaci ’yan siyasa su guji amfani da siyasa wajen zalunci da cin hanci, tare da tabbatar da adalci da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugabannin Kiristoci sun yi kira da a ci gaba da gudanar da addu’o’in neman taimako ga Shugaba Bola Tinubu a Najeriya.

Majiyoyi sun ce addu'ar za ta haɗa da sauran shugabannin siyasa domin fitar da Najeriya daga matsalolin tsaro da tattalin arziki da take fuskanta.

Kiristoci za su yi wa Tinubu addu'a
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a cikin jirgi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

An yi wannan kiran ne a wani taron addu’a na kasa da kungiyar Northern Christian Religious Leaders Assembly (NOCRELA) ta shirya ranar Alhamis a Abuja, cewar PM News.

Kara karanta wannan

'Babban kuskure da ƴan Najeriya za su yi idan suka gujewa zaɓen Tinubu a 2027'

Ana shirin yi wa Tinubu da Najeriya addu'o'i

Taron ya samu halartar shugabannin Christian Association of Nigeria (CAN), Nigerian Christian Pilgrim Commission (NCPC), da wakilan kungiyoyin coci daban-daban.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Sakataren NCPC, Bishop Stephen Adegbite, ya bukaci Kiristoci su tsaya wajen yi wa Shugaba Tinubu addu’a, yana bayyana shi a matsayin shugaban da ke kokarin tabbatar da hadin kan Najeriya da ci gabanta.

Adegbite ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsalolin tattalin arziki, amma ya bayyana fatansa cewa sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa za su haifar da amfani ga kasar nan gaba.

Ya ce:

“Ba kai ne irin mutumin da zai ruguza Najeriya ba; kana gina Najeriya ne."

Shi ma mai shirya taron kuma shugaban NOCRELA, Archbishop JohnPraise Daniel, ya ce duk da matsalar ’yan bindiga, zubar da jini da matsin tattalin arziki, Najeriya za ta iya shawo kan kalubalen da take fuskanta.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Ya jaddada cewa gina kasa ba aikin shugabannin siyasa kadai ba ne, domin kowane dan kasa yana da rawar da zai taka wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba.

Shugaban CAN ya yi magana kan zaman lafiya a Najeriya
Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN a Najeriya, Daniel Okoh. Hoto: Christian Association of Nigeria, CAN.
Source: Facebook

Jawabij shugaban kungiyar CAN a Najeriya

A cikin sakon da ya gabatar, Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya bayyana cewa Najeriya tana cikin wani muhimmin lokaci yayin da harkokin siyasa ke kara karfi gabanin babban zaben 2027.

Daraktan Hulda da Addinai da Sauran Kungiyoyin Addini, Very Rev. Princewill Ireoba, ne ya wakilci Okoh a taron, cewar Leadership.

Okoh ya gargadi ’yan siyasa da kada su yi amfani da siyasa wajen cimma manufofinsu, yana cewa Najeriya na bukatar hikimar Allah, adalci da shugabanci na kwarai fiye da dabarun siyasa kawai.

Ya sake tabbatar da aniyar CAN ta hada kai da NOCRELA da sauran kungiyoyi wajen inganta zaman lafiya, gaskiyar dimokuradiyya da adalci a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya yi huduba ga Musulmai, Kirista

An ji cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya buƙaci Musulmi da Kiristoci su daina aibanta addinan juna.

Mai alfarma Sultan ya gargadi mabiya addinai da kada wani bangare ya dauki kansa cewa ya fi abokin zamansa.

Muhammad Sa’ad III ya jaddada muhimmancin kula da maƙwabta ba tare da la'akari da addininsu ko kabilar da suka fito ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.